Facebook: Kawunan 'yan majalisa sun rabu

Roy Moore Hakkin mallakar hoto CBS

Manyan jami'an kamfanonin fasaha na duniya sun isa birnin Washington domin amsa tambayoyi daga 'yan majalisar kasar Amurka.

A ganawa ta baya-bayan nan, kamfanonin Facebook, da Twitter da YouTube sun fuskanvi tsauraran tambayoyi daga kwamitin shari'a na majalisar game da yadda suke tace bayanai - kuma majalisar tana son sanin ko akwai dalilai na siyasa wajen aiwatar da ayyukan nasu.

A wasu lokuta sai kaji tamkar 'yan majalisar da ke ganawar da kamfanonin fasahar daga wata duniyar suke.

A bangare daya, 'yan jam'iyyar Republican a majalisar sun fi mayar da hakulansu ne akan abin da suka kira 'yunkurin dode muryoyin masu ra'ayin rukau a shafukan sada zumunta'.

Su kuwa 'yan jam'iyyar Democrat gani suke batun kutsen da ake tuhumar Rasha da aikatawa a zaben Amurka na 2016 shi ne yafi muhimmanci.

An shiga rudani a yayin da 'yan majalisar suka nemi bayani game da labaran kanzon kurege da ake bazawa ta shafukan sada zumunta.

Wani shafin intanet mai suna Infowars wanda ke da mabiya fiye da miliyan biyu a Facebook ya rika bayyana wadanda suka tsira da raytukansu a lokutan da 'yan bindiga ke kai hare-hare cikin Amurka a matsayin masu neman suna.

Shugabar sashen tsare-tsare ta Facebook, Monika Bickert ta amsa da cewa Infowars ba su kai munzalin da Facebook za ta rufe shafin nasu ba - kuma ta kasa bayar da wasu dalilai.

Labarai masu alaka