Russia 2018: Dole Super Eagles ta dauki darasi – Iwobi

  • Daga Oluwashina Okeleji
  • BBC Sport, Nigeria
Alex Iwobi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alex Iwobi na daga cikin 'yan wasa marasa shekaru da suka halarci gasar kofin duniya ta bana a Rasha

Dan wasan Najeriya Alex Iwobi, mai shekara 22, ya ce yana fatan 'yan wasan Super Eagles za su koyi darasi daga gasar cin kofin duniya da kuma fatan za su gina kansu domin gaba.

An fidda kasar daga gasar ne bayan Argentina ta doke ta da ci 2-1.

"Yawancin 'yan tawagarmu matasa ne kuma mun dauki manyan darussan da muke fatan za su taimaka mana mu ci gaba," in ji Iwobi.

"Nan gaba kadan hankalin kowa zai koma kan gasar cin kofin kasashen Afirka, kuma dole ne mu dauki darussan gasar cin kofin duniya da mahimmanci sosai."

Kasar ba ta sake samun damar shiga gasar cin kofin Afirka ba tun lokacin da suka lashe gasar a shekarar 2013.

Magoya bayan kasar sun yi fatan cewa Iwobi zai taka muhimmiyar rawa a Rasha, amma sai hakan bai yiwu ba, saboda yadda bai buga cikakken wasa ba a wasanni ukun da kasar ta buga.

"Kocin bai sanya ni cikin wannan wasa ba saboda yana son gwada sabon zubi, don haka ba ni da matsala saboda a karshen abin da manaja ya yanke shawara akai shi zai faru," in ji dan kwallon.

Duk da cewa ya buga kasarsa wasanni 22, Iwobi na daya daga cikin manyan 'yan wasa a cikin tawagar Najeriya wadanda suka kasance mafi kananan shekaru a Rasha.

Iwobi ya wakilci Ingila a wasannin 'yan kasa da shekara 16 da 17 da kuma 18 kafin ya sauya sheka zuwa Najeriya domin ya bi sahun kawunsa wato tsohon kyaftin din Super Eagles Austin Jay-Jay Okocha.

A watan Oktoban shekarar 2015 ne ya fara taka leda a wasan da suka yi da DR Congo a wasan sada zumunci a Vise, a kasar Belgium.