Ina makomar Hazard da Neymar da Zaha da Golovin da Alcantara?

Ousmane Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ousmane Dembele na cikin tawagar Faransa da ta lashe kofin duniya ta 2018

Barcelona ta shirya domin kure Chelsea ta hanyar yi mata tayin dan wasan gaban Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 21, domin musanyensa da dan wasan gaban Belgium mai shekara 27, Eden Hazard, in ji Onda Cero, via Metro.

Dan wasan gaban Crystal Palace dan kasar Ivory Coast, Wilfried Zaha, mai shekara 25, yana gaba-gaba cikin 'yan wasan da Marco Silva yake son ya saya wa Everton, yayin da dan wasan gaban Arsenal da Ingila Danny Welbeck, mai shekara 27, yana daya daga cikin 'yan wasan da Toffees suke so, in ji Mirror.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nabil Fekir shi ma ya ci kofin duniya

Liverpool ta yanke kauna wajen sayan dan wasan tsakiyar Lyon dan Faransa, Nabil Fekir, mai shekara 25, yayin da take neman mai tsaron gidan Roma dan kasar Brazil, Alisson, a cewar Daily Mail..

Sabon kocin Chelsea, Maurizio Sarri, zai so ya sayi 'yan wasan Juventus biyu - dan wasan gaban Argentina, Gonzalo Higuain, mai shekara 30, da kuma dan wasan bayan Italiya, Daniele Rugani, mai shekara 23 - amma wata yarjejeniyar kin kwace 'yan wasan juna na nufin ba zai iya sayen 'yan wasan Napoli da yawa da yake so ba, kamar yadda dan jaridan Evening Standard, Tom Collomosse, ya fada a wani shirin BBC Radio 5 live.

Amma Rugani ya riga ya cimma yarjejeniyar kashin kai da Stamford Bridge, in ji (Sky Sports Italia, via Express).

Dan wasan gaban Brazil, Neymar, mai shekara 26, zai ki amincewa da tayin Real Madrid domin ci gaba da zama a Paris St-Germain - in har suka ci gaba da yi masa rikon alfarma, kamar yadda El Pais ta rawaito.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Aleksandr Golovin ya taka wa Rasha rawar gani a gasar kofin duniyar da ta karbi bakunci

Chelsea tana sahun gaba wajen neman sayen dan wasan tsakiya mai shekara 22, Aleksandr Golovin, daga CSKA Moscow bayan rawar ganin da ya taka a gasar kofin duniyar da aka yi a Rasha, in ji football.london.

Dan wasan bayan Sfaniya, Nacho Monreal, mai shekara 32, zai tsaya a Arsenal a wannan kakar bayan da Real Sociedad ta daina zawarcin dan kwallon, a cewar Mundo Deportivo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Thiago Alcantara kwararran dan kwallo da ya dade yana taka-leda

Arsenal ta kuma shirya domin ayyana wata yarjejeniyar da dan wasan Barcelona mai shekara 16, Joel Lopez, bayan amincewa da sharuddan karatunsa, in ji London Evening Standard..

Manchester United tana tunanin neman 'yan wasan Bayern Munich biyu - dan wasan gaban Poland, Robert Lewandowski, mai shekara 29, da kuma dan wasan tsakiyar Sfaniya Thiago Alcantara, mai shekara 27.

Haka nan kuma tana duba yiwuwar sayen dan wasan bayan Tottenham dan kasar Belgium Toby Alderweireld, mai shekara 29, kamar yadda jaridar Independent ta rawaito.