City za ta sayar da Sterling, William zai bar Chelsea, Navas zai ja da Courtois

Hakkin mallakar hoto Clive Brunskill
Image caption Willian bai ji dadin aiki tare da tsohon kocin Chelsea Antonio Conte a kakar da ta gabata

Manchester City za ta iya sayar da Sterling cikin wata 12 idan ya ki sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya. Dan kwallon na Ingila na da kwantiragi daga nan har shekarar 2020, amma City ba za su bar kwantiragin manyan 'yan wasansu ta kare ba, in ji Daily (Mirror).

Sai dai Sterling na fargabar ba zai samu yarjejeniya mai gwabi ba saboda rashin taka rawar kiki da bai yi ba a gasar kofin duniya da aka kammala, a cewar (Telegraph)

Dan wasan Liverpool da Brazil Fabinho, mai shekara 24, na kokarin shawo kan tsohon abokin wasansa a Monaco Kylian Mbappe ya koma Liverpool da taka leda. Mbappe, mai shekara 19, ya lashe kofin duniya na bana da Faransa, a cewar (Liverpool Echo).

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger shi ne kan gaba a sahun mutanen da ake zaton kasar Japan na nema domin zama kocin kasar. Kocin mai shekara 68 dan kasar Faransa ya ce yana so ya ci gaba aikin koci, kamar jaridar Daily Mail ta ruwaito.

Chelsea za ta nemi golan AC Milan Gianluigi Donnarumma, mai shekara 19, idan mai tsaron gidan Belgium Thibaut Courtois - wanda Real Madrid ke nema - ya bar Stamford Bridge a bana, a cewar (London Evening Standard)

Golan Costa Rica Keylor Navas, mai shekara 31, zai ci gaba da zama a Real Madrid domin kare matsayinsa ko da kuwa Real ta sayi golan Chelsea Courtois, in ji (AS).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daniele Rugani matashin dan wasan baya ne

Dan wasan baya naJuventus da Italy Daniele Rugani, mai shekara 23, zai koma Chelsea kan kwantiragin shekara biyar, inda zai rinka karbar fan 77,000, sannan Chelsea ta biya zakarun na Italiya fan miliyan 44.2, a cewar (London Evening Standard) .

Har yanzu dan wasna tsakiya na Brazil Willian, mai shekara 29, na son barin Chelsea duk da nadin Maurizio Sarri a matsayin koci a Stamford Bridge. Willian bai ji dadin aiki tare da tsohon koci Antonio Conte a kakar ta gabata ba, a cewar (Sun).

Wilfried Zaha ya shiada wa Crystal Palace cewa yana son barin kulob a bana, inda su kuma suka sanya farashin fan miliyan 70 a kan dan kwallon na Ivory Coast, mai shekara 25, kamar yadda (Sun) ta ruwaito.

A shirye Arsenal take ta sayar da Danny Welbeck domin rage 'yan wasanta, kuma rahotanni sun ce Everton za su biya fan miliyan 15, in ji (Sun).

Labarai masu alaka