Liverpool ta sayi sabon gola, Alisson, a kan fam 66m

Alisson Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alisson ne ya kama wa Brazil gola a gasar cin kofin duniya a Rasha

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sayi golan Roma a kan fam miliyan 66.8 (Yuro miliyan 72.5), abin da ya sa ya zama golan da ya fi tsada a duniya.

Alisson, wanda ya kama wa Brazil gola a wasannin da ta buga a gasar cin kofin duniya a Rasha, ya kulla yarjejeniyar shekara shida ne da Liverpool.

Ya sha gaban Gianluigi Buffon wanda a baya shi ne golan da ya fi tsada a duniya, tun bayan da Juventus ta saye shi daga Parma a kan Yuro miliyan 53 a shekarar 2001.

"Game da rayuwata da sana'ata, wannan babban ci gaba ne kasancewata a wannan kungiya," in ji dan kwallon mai shekara 25.

Golan ya koma Roma ne kimanin shekara biyu da suka wuce, inda ya buga wa kungiyar wasa a gasar Serie A a kakar 2017-18.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce sun sayo "hazikin dan wasa."

Ya ce a cikin makonnin da suka gabata ne suka yi tunanin sayo daya daga cikin manyan gololin da duniya take ji da su.

Alisson shi ne dan wasa na hudu da kungiyar ta saya tun bayan kammala Gasar Firimiya, inda ta kare a matsayi ta hudu.

Real Madrid ce ta doke kungiyar a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai da ci 3-1.

Labarai masu alaka