Real Madrid ta sayi matashin dan wasan Brazil Vinicius

Vinicius de Oliveira Júnior Hakkin mallakar hoto Real Madrid

Real Madrid ta sayi matashin dan wasan Brazil Vinicius de Oliveria Júnior daga kulob din Flamengo.

Ana yi wa Vinicius mai shekara 18 kallon na daya daga cikin matasan da suka fi haskakawa a fagen wasan kwallon kafa a duniya.

Dan wasan gaban ya koma Madrid ne bayan ya buga wa Flamengo na Brazil wasa 70, inda ya ci kwallo 14.

Vinicius ya buga wasansa na farko ne a ranar 13 ga watan Mayun 2017 a wasan da suka kece raini da Atlético Mineiro.

Ya kuma taka-leda a gasar zakarun Latin Amurka ta Copa Libertadores da kuma gasar cin kofin Amurka ta kudu, inda yaci kwallaye a duka.

A bara ya lashe kofin kasashen Latin Amurka na 'yan kasa da shekara 17 tare da Brazil, inda ya zura kwallo bakwai, sannan aka zabe shi gwarzon dan wasa a gasar.

Wani sako da Real Madrid ta wallafa a shafinta na intanet, ya bayyana Vinicius da cewa mai hazaka ne, ga sauri kamar walkiya, kuma ya kasance dodon raga, don haka sai ya fita daban a cikin Flamengo da kuma tawagar matasa ta Brazil.

Hakkin mallakar hoto Real Madrid/Twitter
Image caption Vinicius de Oliveria Júnior zai so ya bi sahun manyan 'yan wasan Brazil irinsu Ronaldo da suka yi fice a duniya

Labarai masu alaka