An dage wa AC Milan haramcin buga gasar Europa

shugaban AC Milan Marco Fassone Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Uefa ta hukunta AC Milan ne saboda ta kashe fan miliyan 200

An dage haramcin shekara daya na buga wasannin gasar Turai a kan AC Milan.

Hukumar Uefa ce ta zartar da hukuncin a kan Milan saboda ta keta dokar cinikin 'yan wasa bayan ta kashe fan miliyan dari biyu a kasuwar musayar 'yan wasa.

Amma kotun wasanni (Cas) ta yi watsi da hukuncin inda ta amince da karar da AC Milan ta daukaka.

Yanzu hukuncin kotun ya ba AC Milan damar buga wasannin gasar Europa League a bana.

An kammala Seria A, Milan tana matsayi na shida, wanda ya ba ta damar buga matakin rukuni na gasar Europa League.

Yadda hukuncin yake tun farko

Kulub din ya kasance mallakin tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi daga 1986 kafin sayar wa wasu 'yan China kan yuro miliyan 740 a watan Afrilun 2017.

A lokacin kulub din ya kashe fan miliyan dari biyu wajen sayen 'yan wasa, da suka hada da Leonardo Bonucci daga Juventus da Andre Silva daga FC Porto.

Kotun wasanni ta ce duk da cewa hukuncin Uefa ya yi daidai amma ya kasa cimma wasu sharudda wadanda ya kamata a yi la'akari da su.

Cas ta ce arzikin kulub din yanzu ya fi na da.

An dai bullo da dokar kashe kudi wajen sayen 'yan wasa domin kaucewa durkushewar kungiyoyin kwallon kafa a Turai.

Kulub na iya fuskantar hukunci idan da ya kashe kudi fiye da adadin kudaden da yake samu.

Hukuncin ya shafi gargadi ko rage maki ko kuma takunkumin sayen 'yan wasa.

Labarai masu alaka