Andres Iniesta da Fernando Torres sun shiga Japan da kafar hagu

Andres Iniesta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andres Iniesta bai taba taka-leda a wani kulob banda Barcelona ba

Kwararrun 'yan kwallon Spaniya Andres Iniesta da Fernando Torres duk sun sha kayi a wasanninsu na farko da suka buga a gasar J-League ta kasar Japan.

Iniesta, wanda ya lashe kofuna 32 a Barcelona, ya shigo wasa ana saura minti 32 a tashi a karawar da Vissel Kobe ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Shonan Bellmare.

Da dama daga cikin 'yan kallo 26,000 da ke filin wasan sun rinka daga tutar Spain saboda dan wasan mai shekara 34 da haihuwa.

Tsohon dan wasan gaba na Chelsea da Liverpool Torres shi ma bayan an dawo hutun rabin lokaci aka saka shi a wasan da Sagan Tosu ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gida a hannun Vegalta Sendai.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fernando Torres ya ci kwallo biyu a wasansa na karshe a Atletico Madrid sai dai ba ya cikin tawagar Spain ta gasar kofin duniya

Torres, wanda shi ma shekararsa 34, ya bar Atletico Madrid a bana bayan ya zura kwallo 129 a wasa 404 da ya yi a karo biyu da ya zauna a kungiyar.

Kulob dinsu Torres yana fuskantar kalubalen faduwa zuwa karamar gasar Lig.

Wannan ne wasan farko da Iniesta ya buga wa wani kulob a rayuwarsa bayan Barcelona - inda ya take-leda sau 674 - ko kuma Spain.

Ya yi ritaya daga wasannin kasa-da-kasa bayan da aka fitar da Spain a gasar kofin duniya ta Rasha 2018.

Labarai masu alaka