Na yi hoto da shugaban Turkiya ne don girmama asali na - Ozil

lkay Gundogan and Mesut Ozil, along with Everton's Cenk Tosun, pose with the Turkish president Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ilkay Gundogan da Mesut Ozil, da Cenk Tosun na Everton tare da shugaban Turkiya

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya ce kin wallafa hotonsa tare da shugaban Turkiya zai kasance rashin girmamawa ga asalinsa.

Ozil da Ilkay Gundogan na Manchester City dukkaninsu jamusawa kuma 'yan asalin Turkiya sun sha suka daga hukumar kwallon Jamus bayan ganawarsu da Recep Tayyip Erdogan a watan Mayu.

A cikin wata sanarwa, Ozil ya ce, "ziyarar ba ta shafi siyasa ba ko wani zabe."

"Ina da zuciya biyu, daya a Jamus daya kuma a Turkiya", kamar yadda Ozil ya wallafa a Twitter.

"Wannan ni ya shafa na wakiltar ofishi mafi girma a kasar iyaye na."

Ozil ya ce lokacin da yana karami, mahaifiyarsa ta horar da shi a kullum ya kasance mai girmamawa kuma kada ya taba manta asalinsa.

Daga baya kuma Ozil ya sake wallafa wani sako yana mai kalubalantar kafofin watsa labaran Jamus da suka dauki laifin rashin nasarar da kasar ta yi a gasar cin kofin duniya suka dora a kan hotunansa da shugaban Turkiya.

Ya ce "ba su soki rawar da na taka ba da kuma tawagarmu ba amma sun soki asali na da kuma yadda nake girmama shi.

"Wannan ya keta iyakar da bai kamata a keta ba, inda jaridu suka nemi dora alhakin kasar Jamus a kai na."

Bayan dan wasan ya gana da Erdogan a wani taro a London, inda Ozil ya ce sun tattauna game da kwallon kafa, sai jam'iyyar AK mai mulki a Turkiya ta wallafa hotuna ana dab da zaben da Erodogan ya lashe.

'Yan siyasar Jamus da dama sun soki Ozil da Gundugan, suna masu bayyana shakku kan amincinsu ga mutunta tsarin dimokuradiyar Jamus.

Jamus ta soki shugaba Erdogan kan yadda yake murkushe abokan hamayyar siyasa bayan murkushe wani yunkuri na yi ma sa juyin mulki.

Ozil ya ce ba ruwansa da wanda ke shugaban kasa, ko dan Turkiya ne ko Jamus, tunaninsa ba zai sauya ba.

Labarai masu alaka