Mece ce makomar Martial da Rojo da dan wasan tsakiyar Madrid?

Anthony Martial Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea na hakon dan wasan Man United Anthony Martial

Chelsea na tunani akan ko ta karbi fan miliyan 65 da Barcelona ta taya dan wasan tsakiya Willian, yayin da Manchester United ke shaukin sayen dan wasan mai shekara 29, in ji Mail.

Har wa yau Chelsea suna son sayen dan wasan gaban Manchester United dan asalin kasar Faransa, Anthony Martial, mai shekara 22, a cewar Talksport.

Dan wasan tsakiyar Real Madrid, Mateo Kovacic, na son barin kulob din domin samun damar taka-leda, inda Bayern Munich da Juventus da Liverpool da Manchester City da kuma Manchester United ke son sayen dan kwallon dan asalin kasar Croatia mai shekara 24, in ji Marca.

Fulham ta shiga takara da Lazio wajen sayen dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 27, Andre Schurrle, wanda aka bai wa Crystal Palace da Everton, in ji Mail.

Da alama dan wasan bayan Argentina, Marcos Rojo, mai shekara 28, shi ne dan wasan da za a sayar idan United ta samu ta sayi dan wasan bayan Ingila Harry Maguire, mai shekara 25, daga Leicester City, kamar yadda Mirrorta rawaito.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tattaunawar Liverpool da Domagoj Vida na zuwa ne a lokacin da ake cewa damarta ta sayen dan wasan dan Faransa, Nebil Fekir, ta kare

Crystal Palace da Fulham suna takara da Tottenham wajen sayen dan wasan tsakiyar Ingila Jack Grealish kuma sun tuntubi Aston Villa game da ciniki cikin 'yan kwanakin nan, in ji Mirror.

Da alama damar Liverpool ta sayen dan wasan tsakiyar Lyon kuma dan kasar Faransa Nabil Fekir ta kare inda rahotanni a Faransa ke cewa yarjejeniyar ba za ta auku ba, a cewar Express.

Duk da haka, kungiyar ta Anfield ta shirya domin tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya Besiktas cikin kwanaki masu zuwa domin sayen dan wasan bayan Croatia, Domagoj Vida, mai shekara, 29, in ji Star.

Sabon kulob din gasar Firimiya Wolves na kan tattaunawa da dan wasan Portugal mai shekara 31 Joao Moutinho domin sayo shi daga Monaco kan kudi fan miliyan 6 cikin wannan makon, a cewar Mail.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sabon mai tsaron gidan Liverpool dan kasar Brazil, Alisson Becker, mai shekara 25, ya shirya domin ya fara taka-leda a kulob din a wani wasan sada zumunta na shirya wa kakar gasar Firimiya inda za ta kara da Napoli a Dublin ranar Asabar, 4 ga watan Agusta, in ji jaridar Telegraph.

Shugaban kungiyar kwallon kafa taNapoli Aurelio de Laurentiis ya ce kungiyar tana sha'awar sayen dan wasan bayan Manchester United dan Italiya, Matteo Darmian, mai shekara 28, a cewar Sun.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yerry Mina ya taka rawar gani a gasar kofin duniyar da aka kammala a watan Yuli

Dan wasan bayanBarcelona dan Colombia, Yerry Mina, mai shekara 23, ya shirya domin komawa gasar Firimiya inda ake kyautata zaton cewa kungiyar Everton ce za ta saye shi, a cewar shafin Goal.

Rahotanni sun ce Juventus ta taya dan wasan bayan Brazil Alex Telles, kan kudi fan miliyan 26.8 daga Porto, sai dai kuma kungiyar ta Portugal ta hakikance akan kudin fansa na fan miliyan 35.7, in ji Football Italia.

Dan wasan tsakiyar Manchester City, dan kasar Ukrain, Oleksandr Zinchenko, mai shekara 21, ya ce shi bai san makomarsa ba a kulob din da ke rike da kofin gasar Firimiya, kamar yadda Manchester Evening News ta rawaito.

Karanta karin labaran musayar 'yan kwallo

Labarai masu alaka