Ba zan sake buga wa Jamus kwallo ba - Mesut Ozil

lkay Gundogan and Mesut Ozil, along with Everton's Cenk Tosun, pose with the Turkish president Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ilkay Gundogan da Mesut Ozil, da Cenk Tosun na Everton tare da shugaban Turkiyya

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya yi ritaya daga buga wa Jamus kwallon kafa yana mai cewa an nuna masa banbancin launin fata tare da cin zarafinsa saboda ya dauki hoto da shugaban kasar Turkiyya.

An soki dan wasan mai shekara 29 bayan ya dauki hoto da Shugaba Recep Tayyip Erdogan a wurin wani taro a Landon a watan Mayu.

Ya ce an rinka tura masa da sakonnin cin mutrunci da nuna kiyayya, sannan aka dora masa alhakin mummunar rawar da Jamus ta taka a gasar kofin duniya.

"Ni dan kasar Jamus ne a wurinsu a lokacin da muka yi nasara, amma ni dan ci-rani ne idan muka sha kashi," a cewar Ozil.

Hukumar kwallon kafa ta Jamus ta yi watsi da zargin wariyar launin fatar Mesut Ozil, sai dai kuma ta ce "ba ta dauki matakin da ya dace wurin kare shi daga cin zarafi ba".

An haifi dan kwallon ne wanda ya fito daga tsatson Turkawan da suka yi kaura zuwa Jamus a garin Gelsenkirchen, kuma yana cikin tawagar kasar da ta lashe gasar kofin duniya a 2014.

Ya buga wa kasar wasa sau 92 sannan sau biyar magoya baya na zabarsa gwarzon dan kwallon kasar tun daga shekarar 2011.

Sai dai tawagar kasar ta kasa kai wa zagaye na biyu a gasar kofin duniya ta Rasha, duk da cewa suna daya daga cikin wadanda aka yi hasashen za su lashe kofin.

Asalin sabanin

Ozil da Ilkay Gundogan na Manchester City dukkaninsu jamusawa kuma 'yan asalin Turkiyya sun sha suka daga hukumar kwallon kafa ta Jamus bayan ganawarsu da Recep Tayyip Erdogan a watan Mayu.

A cikin wata sanarwa, Ozil ya ce, "ziyarar ba ta shafi siyasa ba ko wani zabe."

"Ina da zuciya biyu, daya a Jamus daya kuma a Turkiyya", kamar yadda Ozil ya wallafa a Twitter.

"Wannan ni ya shafa na wakiltar ofishi mafi girma a kasar iyaye na."

Ozil ya ce lokacin da yana karami, mahaifiyarsa ta horar da shi a kullum ya kasance mai girmamawa kuma kada ya taba manta asalinsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mesut Ozil ya bai wa Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan rigarsa ta Arsenal ta musamman wacce ya sanya wa hannu

Daga baya kuma Ozil ya sake wallafa wani sako yana mai kalubalantar kafofin watsa labaran Jamus da suka dauki laifin rashin nasarar da kasar ta yi a gasar cin kofin duniya suka dora a kan hotunansa da shugaban Turkiya.

Ya ce "ba su soki rawar da na taka ba da kuma tawagarmu ba amma sun soki asali na da kuma yadda nake girmama shi.

"Wannan ya keta iyakar da bai kamata a keta ba, inda jaridu suka nemi dora alhakin kasar Jamus a kai na."

Bayan dan wasan ya gana da Erdogan a wani taro a Landan, inda Ozil ya ce sun tattauna game da kwallon kafa, sai jam'iyyar AK mai mulki a Turkiyya ta wallafa hotuna ana dab da zaben da Erodogan ya lashe.

'Yan siyasar Jamus da dama sun soki Ozil da Gundugan, suna masu bayyana shakku kan amincinsu ga mutunta tsarin dimokuradiyar Jamus.

Jamus ta soki shugaba Erdogan kan yadda yake murkushe abokan hamayyar siyasa bayan murkushe wani yunkuri na yi ma sa juyin mulki.

Ozil ya ce ba ruwansa da wanda ke shugaban kasa, ko dan Turkiyya ne ko Jamus, tunaninsa ba zai sauya ba.

Labarai masu alaka