Real Madrid ta sayi sabon gola

Lunin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andriy Lunin

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sayi sabon gola Andriy Lunin daga kungiyar Zorya Luhansk.

Dan wasan mai shekara 19 zai koma Madrid daga kungiyar Zorya Luhansk a kan yarjejeniyar shekara shida.

Golan wanda dan kasar Ukraine ne yana taka wa tawagar kasar teda, kuma sau 40 yana buga wa kungiyarsa wasa a gasar firimiyar kasar.

A makon jiya ne Madrid ta sayi matashin dan wasan Brazil Vinicius de Oliveria JĂșnior daga kulob din Flamengo.

Ana yi wa Vinicius mai shekara 18 kallon na daya daga cikin matasan da suka fi haskakawa a fagen wasan kwallon kafa a duniya.

Labarai masu alaka