Ba a yi wa Mesut Ozil adalci ba – Erdogan

Recep Tayyip Erdogan da Mesut Ozil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ozil da Shugaba Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya goyin bayan Mesut Ozil kuma ya ce "wariyar launin fatar" da aka nuna masa ba daidai ba ne."

An rika sukar dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal, mai shekara 29, bayan da aka dauki hotonsa da Shugaba Erdogan a wani taro da aka yi a birnin Landan a watan Mayu da ya gabata.

Ozil ya yi ritaya ne daga bugawa tawagar kasar Jamus wasa, inda ya ce an rika nuna masa "wariya da rashin mutunci" kan tsatsonsa na Turkawa.

Hukumar kwallon kafa ta Turkiyya (TFF) ta yi tayin mara wa "Mesut Ozil da iyalansa baya".

Hukumar ta TFF a cikin wata sanarwa ta ce: "Mun yi Allah-wadai kan yadda aka rika yi wa Ozil barazanar da kuma sakonin batanci da aka rika tura masa saboda asalinsa."

"Kowane dan wasa, ko da suna gaban jama'a ko kuma a'a. Suna da hakkin a ba su kariya daga cin zarafi da wariya da kuma sakonin nuna kiyayya."

Erdogan ya kara da cewa: "A daren Litinin na yi magana da Mesut. Bayanin da ya yi cikin sanarwar da ya fitar ya nuna cewa yana kishin kasarsa."

"Ba a yi adalci ba idan aka amince da wariyar da aka nuna wa matashin da ya taka rawa sosai a nasarar da tawagar Jamus ta samu. Sam be kamata a lamunta da wannan ba."

A cikin wata doguwar sanarwa da Ozil ya fitar a ranar Litinin, ya ce an rika tura masa da sakonnin kiyaya da barazana kuma an dora alhakin rashin tabuka wani abin azo a gani da tawagar Jamus ta yi a gasar kofin duniya a kansa.

An haifi Ba'amushen dan asalin kasar Turkiyya a garin Gelsenkirchen kuma yana cikin 'yan wasan da suka nuna kwazo sosai a tawagar da ta dauki kofin duniya ta FIFA a shekarar 2014.

Ya rike mukamin kyaftin sau 92 kuma sau biyar magoya baya suka zabe shi a matsayin dan wasan da ya nuna bajinta a tawagar kwallon kafar kasar tun daga shekarar 2011.

"Ni Ba'jamushe ne idan na yi nasara, amma ni bakin haure idan mun sha kaye," in ji Ozil.

"A baya na rika alfahari da rigar Jamus amma yanzu ko a jikina."

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba