Mece ce makomar Lloris da Martial da kuma Higuain?

Hugo Lloris

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid na tunanin taya mai tsaron gidan Tottenham da kuma Faransa, Hugo Lloris, mai shekara 31, kan kudi fan miliyan 60, in ji (Sun).

Attajirin nan dan Rasha, Alisher Usmanov, na kokarin sayar da hannun jarinsa na kashi 30 cikin 100 na kungiyar kwallon kafa a Arsenal, bayan ya amince da cewa mutumin da ya fi hannun jari a kungiyar Stan Kroenke ba zai sallamar ma sa mafi rinjayen hannun jarin kungiyar ba, in ji (Financial Times).

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da kuma Chelsea sun yi tambaya game da dan wasan tsakiyar Bayern Munich da Sifaniya, Thiago Alcantara, mai shekara 27, wanda za a iya sayarwa kan kudi fan miliyan 62, (ESPN).

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United tana neman wani dan wasan da za su saya maimakon dan wasan Chelsea dan kasar Brazil Willian, mai shekara 29, kuma tana hakon dan wasan Eintracht Frankfurt dan asalin kasar Croatia, Ante Rebic, mai shekara 24, in ji (Independent).

Barcelona ta sayi dan wasan tsakiyar Bordeaux Malcom, mai shekara 21, bayan Chelsea ta ki tayin fan miliyan 44 da kungiyar ta Kataloniya ta yi wa Willian, in ji (Mundo Deportivo - in Spanish).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bordeaux ta ki sayar wa Chelsea Malcom

Tottenham da Chelsea za su iya zawarcin dan wasan Faransa Anthony Martial, mai shekara 22, wanda yake son ya bar Manchester United, amma kuma yana son ya ci gaba da taka leda a gasar Firimiya, in ji (Sun).

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea za ta iya rasa dan wasan gaban Juventus Gonzalo Higuain, mai shekara 30, yayin da abokiyar hamayyarta ta gasar Serie A, AC Milan, take son sayen dan wasan dan kasar Argentine kan kudi fan miliyan 57, in ji (Evening Standard).

Chelsea ta kusa sayen golan Ingila Robert Green, mai shekara 38, domin maye gurbi a wani cinikin dan wasa mai cike da mamaki, in ji (Sun).

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ba ya son sayen dan wasan tsakiyar Juventus dan asalin Bosniya, mai shekara 28 Miralem Pjanic, in ji (RMC Sport).

Liverpool ba za ta sayar da dan wasan gaban Ingila, Daniel Sturridge, mai shekara 28 ba a wannan kakar, amma a shirye suke su sayar da shi a kasuwar musayar 'yan wasa ta lokacin bazara mai zuwa, in ji (Liverpool Echo).