Mata ta haifi 'yan biyar da kanta a Filato

Ma'auratan da suka haifi jarirai biyar
Bayanan hoto,

Alhaji Garba Dan Ja Wase da mai dakinsa Hajiya Jamila

Wasu ma'aurata sun haifi jarirai 'yan biyar a wani asibiti da ke Jos babban birnin jihar Filato.

A ranar Litinin ne da ta gabata mai dakin Alhaji Garba Dan Ja Wase ta haifi jariran biyar - maza uku, mata biyu.

Sai dai daga bisani biyu daga cikin mazan uku sun rasu, amma mahaifiyar da sauran jariran da suka rage suna cikin koshin lafiya.

Alhaji Wase ya shaida wa BBC cewa shi da matarsa Hajiya Jamila ba su taba tunanin haihuwar jarirai biyar ba, saboda likitoci sun kasa tantance yawan jariran da ke cikinta a lokacin da take da juna biyun.

Mahaifin jariran ya ce: "Na yi farin ciki kwarai da gaske. Mun gode wa Allah da Ya ba mu haihuwar",

Ya ce ya auri Hajiya Jamila kimanin shekara bakwai da suka gabata ne, sai dai tun bayan wannan lokaci ba su samu rabo ba.

Sai yanzu da Allah Ya albarkace su da jariran, amma ta ce ta haifi yara bakwai da tsohon mijinta.

Ya kuma ce ya rungumi kaddara game da rasuwar biyu daga cikin jariran.