Shin wa zai lashe kyautar Ballon d'Or a bana?

Messi da Modric da Griezmann da Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Modric da Griezmann da Mbappe na iya doke Ronaldo da Messi a Ballon d'Or

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi na cikin sahun 'yan wasa 10 da Fifa za ta zabi gwarzon dan wasan duniya na bana.

Antoine Griezmann da Kylian Mbappe da kuma Raphael Varane da suka lashe wa Faransa kofin duniya suna cikin wadanda ke neman lashe kyautar.

Akwai kuma Luka Modric dan wasan Real Madrid da ya jagoranci Croatia zuwa wasan karshe a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Sai dai Neymar na Brazil ba ya cikin jerin 'yan wasan guda 10 da Fifa za ta zabi gwarzo a bana.

Messi da Ronaldo ne suka mamaye kyautar a tsawon shekaru 10, amma ana ganin a bana ana iya samun sauyi.

Wasu na ganin yadda Messi da Ronaldo suka kasa taka rawar gani a gasar cin kofin duniya a kasashensu, na iya bude kofa ga Antoine Griezmann da Kylian Mbappe da kuma Luka Modric.

Antoine Griezmann shi ne wanda ya lashe kofin duniya ya kuma taimaka wa Atletico Madrid lashe Europa League.

Modric ma na da damar lashe kyautar a bana saboda rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya da kuma taimakawa Real Madrid lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere.

Modric ne ya karbi kyautar gwarzon dan wasa a gasar cin kofin duniya.

Zai kasance karon farko da za a samu wani dan wasa da ya ratso tsakanin Ronaldo da Messi ya lashe babbar kyautar a kwallon kafa.

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai kuma Ronaldo wanda ya karbi kyautar sau biyu a jere, na iya lashe kyautar a karo na uku a jere bayan ya taimakawa Real Madrid kare kofin Zakarun Turai karo uku a jere.

Duk da cewa Messi ya lashe La Liga da Copa de Ray kuma wanda ya fi yawan zura kwallo a raga a Turai a kakar da ta gabata, amma rashin taka rawar gani a gasar cin kofin duniya zai iya hana wa kaftin din na Argentina da Barcelona lashe kyautar a karo na shida.

'Yan wasa 10 da ke takarar gwarzon duniya

  • Cristiano Ronaldo (Portugal) - Real Madrid
  • Kevin De Bruyne (Belgium) - Manchester City
  • Antoine Griezmann (Faransa) - Atletico Madrid
  • Eden Hazard (Belgium) - Chelsea
  • Harry Kane (Ingila) - Tottenham Hotspur
  • Kylian Mbappe (Faransa) - Paris Saint-Germain
  • Lionel Messi (Argentina) - Barcelona
  • Luka Modric (Croatia) - Real Madrid
  • Mohamed Salah (Masar) - Liverpool
  • Raphael Varane (Faransa) - Real Madrid

Fifa za ta tace 'yan wasan zuwa uku a watan Satumba wadanda za a zabi gwarzo daga cikinsu.

Tuni aka fara jefa kuri'a a shafin FIFA.com, har zuwa 10 ga Agustan 2018 da za a rufe kada kuri'a.

Tsarin jefa kuri'a

Masoya kwallon kafa na cikin wadanda ke taka rawa wajen zaben gwarzon duniya da gwarzon koci a bangaren maza da mata.

Haka kuma tsarin zaben gwarzon dan wasan na duniya ya kunshi masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa da suka hada da kaftin da masu horar da 'yan wasa da kuma 'yan jarida.

An rarraba yadda bangarorin za su kada kuri'a.

Kaftin na tawagogin kasashen duniya suna da kashi 25 na kuri'a.

Masu horar da 'yan wasa suna da kashi 25.

Masoya kwallon kafa da suka kada kuri'a a shafin fifa suna da kashi 25.

Sai kuma rukunin 'yan jarida 200 da aka ware wa kashi 25.