Rasha 2018: Pavard ya doke Musa a kwallo mafi shahara a raga

Benjamin Pavard

Asalin hoton, FIFA

Bayanan hoto,

Yadda Benjamin Pavard ya ci kwallon da ta fi shahara a ragar Argentina

Kwallon da Benjamin Pavard na Faransa ya ci Argentina daga nesa aka zaba mafi shahara a raga a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha.

Dan wasan na baya ya lashe kyautar ne bayan ya samu rinjayen kuri'un miliyoyan masoya kwallon kafa da suka kada kuri'a a shafin Intanet na Fifa.

Ana ganin Pavard ya yi amfani da kwarewa wajen harba kwallon daga gefe har ta fada ragar Argentina.

"Ban yi tunanin haka ba. Na yi kokari na kai ga kwallon na ajiye ta," in ji Pavard, mai shekara 22 bayan kammala wasan.

Faransa ta lashe kofin duniya karo na biyu bayan ta doke Croatia 4-2 a wasan karshe da suka fafata a Rasha.

Parvard ya ce kwallon ta taba kasa lokacin da ta zo. "Na yi kokarin harba kwallon daga inda ta fito, kamar yadda maciya raga suke yawan fada."

"Na ji dadi sosai lokacin da kwallon ta shiga raga."

Kwallon da Juan Quintero na Colombia ya ci a bugun tazara ita ce ta zo ta biyu.

Kwallon da Luka Modric ya ci Argentina daga nesa ita ce ta zo ta uku.