Ana cinikin Maguire da Rebic da Vida da Courtois da kuma Mina

Harry Maguire Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harry Maguire

Manchester United ta shaida wa Leicester City tana son sayen dan wasan bayan Ingila da aka kiyasta cewar zai kai fan miliyan 65, Harry Maguire, mai shekara 25, in ji (Mirror).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ante Rebic

United ta fara tuntunba da nufin sayen dan wasan Eintracht Frankfurt mai shekara 24, kuma dan kasar Croatia, Ante Rebic, in ji (Mail).

Liverpool ta cimma yarjejeniyar shekara biyu da dan wasan bayan Croatia, Domagoj Vida, mai shekara 29, amma dole ta iya biyan fan miliyan 22 da Besiktas ke nema, in ji (A Spor - ta Turkiya).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Thibaut Courtois

Real Madrid ta cimma matsaya da golan Chelsea dan asalin Belgium mai shekara 26, Thibaut Courtois, in ji (Mail).

Chelsea da Roma suna takarar sayen dan wasan Jamaica, Leon Bailey, mai shekara 20, daga Bayer Leverkusen, in ji (Evening Standard).

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea na sa ido kan dan wasan tsakiyar Lazio da Serbia, Sergej Milinkovic-Savic, domin taya dan wasan mai shekara 23, in ji (Independent).

Wakilin din Daniele Rugani ya ce Blues na son dan wasan bayan Juventus ta Italiya mai shekara 23, in ji (Radio Sportiva).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wilfried Zaha

Crystal Palace na tattaunawa da dan wasan tsakiyar West Ham dan kasar Senegal, Cheikhou Kouyate, mai shekara 28, kan kudi fan miliyan 10, in ji (Sky Sports).

Kazalika dan wasan Palace kuma dan kasar Ivory Coast, mai shekara 25, Wilfried Zaha, yana neman barin kulob din, in ji (Standard).

Real Madridna nazarin taya dan wasan gaban Paris St-Germain kuma dan kasar Uruguay, Edinson Cavani, mai shekara 31, kan kudi fan miliyan 89, domin maye gurbin Cristiano Ronaldo na Portugal, wanda ya koma Juventus, in ji (AS - Spain).

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Newcastle ta kusa sayen dan wasan Mainz kuma dan kasar Japan mai shekara 26, Yoshinori Muto, in ji (Kicker - ta Jamus).

Labarai masu alaka