Liverpool ta doke Manchester City a Amurka

Sadio Mane scores a penalty for Liverpool against Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya yabawa yunkurin 'yan wasansa bayan da Liverpool ta doke su a wasan sada zumunci

Mohamed Salah ya ci gaba daga inda ya tsaya a kakar da gabata, inda babu bata lokaci ya zura kwallo a raga yayin da Liverpool ta doke Manchester City 2-1 a New Jersey.

The Egypt forward, who scored 44 goals in 52 games for the Reds last season, equalised Leroy Sane's second-half goal barely a minute after coming on as a substitute in front of a 52,000 crowd.

Dan wasan na Masar wanda ya zura kwallo 44 a wasanni 52 a kakar da ta gabata, ya rama kwallon da Leroy Sane ya zira minti daya kacal da shigowarsa fili bayan dawo daga hutun rabin lokaci, a gaban 'yan kallo mutum 52,000.

Salah ya sake kai hari da ka amma kwallon ta doki tirken raga.

Kwallon da Saliyo Mane ya zura a raga da bugun fanareti ana dab da tashi ita ce ta bai wa Liverpool nasara a gasar International Champions Cup.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabon dan wasan Manchester City Riyad Mahrez (hagu) ya buga karawar da Liverpool

Salah da dan wasan Senegal Mane na yi wasa ne a karon farko tun bayan da aka fitar da kasashensu daga gasar cin kofin duniya a zagayen farko.

Dan wasan City Bernardo Silva wanda aka fitar da kasarsa ta Portugal a zagaye na biyu - ya buga wasan farko a kakar wasa ta bana, amma har yanzu City har yanzu City suna wasa ne ba tare da 'yan wasa 15 da suka je Rasha.

"Ba shakka mun yi kokari sosai da 'yan wasan da muke da su a tsawon minti 75 da muka fafata da kungiyar da ta halarci wasan karshe na gasar zakarun Turai," in ji kocin City Pep Guardiola bayan wasan.

Labarai masu alaka