Sa Mourinho murmushi na cikin burin rayuwata - Klopp

Jose Mourinho da Jurgen Klopp Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho ya ce Liverpool za ta lashe kofin Premier

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce "daya daga cikin babban burinsa na rayuwa shi ne ya sa Mourinho murmushi" bayan kocin na Manchester ya ce Liverpool ce za ta lashe kofin Premier a kakar da za a soma.

Mourinho dai har ya sadaukar da kofin Premier ga Liverpool, saboda ta kashe fan miliyan 170 wajen cefanen 'yan wasa.

Amma Klopp ya yi watsi da ikirarin na Mourinho a yayin da suke shirin haduwa da juna a wasan sada zumunci na share fagen kaka a Michigan.

Ba ni da matsala da Mourinho," in ji Klopp.

"Mu muke da hakki da magoya bayanmu da wadanda muke wa aiki. Ni ba ni da sha'awa da Man Utd."

Kalaman Klopp na zuwa ne bayan tsokacin da Mourinho ya yi kan Liverpool cewa tana iya kafa tarihi a kakar bana bayan ta kashe kusan fan miliyan dari biyu da hamsin tsakanin shekara daya.

Kudaden da Liverpool ta kashe sun hada da cinikin £66.8m da ta karbo Alisson golan Roma da kuma £75m da Kloop ya ware ya sayo dan wasan baya Virgil van Dijk daga Southampton a watan Janairu.

Liverpool ta kuma karbo Naby Keita daga RB Leipzig kan kudi da suka kai £50m da kuma Fabinho na Brazil da ta sayo daga Monaco kan kudi da suka kai £40m, sai kuma dan wasan gaba Xherdan Shaqiri da ta karbo daga Stoke kan kudi £13m.

Liverpool dai ta samu kudin cefanen 'yan wasan ne daga kudaden da Barcelona ta biya ta karbi Philippe Coutinho £142m.

Da aka tambayi Mourinho game da kudaden da Liverpool ta kashe sai ya ce: "Bai ga wata kungiyar da ta yi kusa da kashe wadannan kudaden ba - kungiyar da ta kai wasan karshe a gasar zakarun Turai, dole ka ce ta fi damar lashe kofin premier.

Amma da aka tambayi Klopp, ya ce bai yi tunanin zai iya lashe Premier ba, yana mai cewa ya danganta da irin yadda suka taka leda.