Mece ce makomar Willian da Courtois da Maguire da Rojo da Ramsey?

Manchester United manager Jose Mourinho

Asalin hoton, Kevork Djansezian

Halayyar da kocin Manchester United Jose Mourinho ya nuna a ziyarar da kulob dinsa yake a Amurka yana karya gwiwar 'yan wasa tare da tayar da hankalin wadansu ma'aikatan kungiyar, in ji (Mail).

Real Madrid ba ta sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Chelsea, Willian, mai shekara 29, suna son golan Blues ne, dan kasar Belgium, Thibaut Courtois, mai shekara 26, kamar yadda (Marca) ta bayyana.

Willian ya ce yana "matukar jin dadi a Chelsea" kuma yana jin dadin zama a Landan, a cewar Globo Esporte.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Thibaut Courtois

Kocin Leicester Claude Puel, ya jaddada yadda yake jin dadin wasan dan kwallon bayan Ingila, mai shekara 25, Harry Maguire - wanda aka alakanta da Manchester United -zai tsaya da Foxes a sabuwar kaka, in ji (Sky Sports).

Leicester za ta bai wa Maguire sabon kwantiragi, inda za a kara albashinsa daga fan 50,000 zuwa fan 95,000, a cewar (Mirror).

Everton tana son dan wasan Manchester United kuma dan kasar Argentina, mai shekara 28, Marcos Rojo, wanda aka ce an yi cinikinsa a kan kudi fan miliyan 30, in ji (Mirror).

Kocin Chelsea Maurizio Sarri yana zawarcin dan wasan Bayern Munich kuma dan kasar Poland, Robert Lewandowski, mai shekara 29, kamar yadda (Star) ta bayyana.

Ta yiwu Tottenham ba za ta sayi ko wane dan kwallo ba kafin a rufe kasuwar saye da musayar 'yan wasa, kamar yadda koci Mauricio Pochettino ya shaida wa jaridar (Mail).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sadio Mane

Liverpool na da kwarin gwiwar cewa dan wasan gaban Senegal Sadio Mane, mai shekara 26, zai sanya hannu kan wata yarjejeniya mai tsawo cikin makonni masu zuwa, in ji (Mirror).

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta fara tattaunawa dan wasan tsakiyar Inter Milan dan kasar Uruguay, Matias Vecino, mai shekara 26, kuma ta yi wa Juventus tayin fan miliyan 35.5 kan dan wasan bayan, mai shekara 24, Mattia Caldara, in ji (London Evening Standard).

Har ila yau Chelsea tana tunanin sayan dan wasan Arsenal Aaron Ramsey, mai shekara 27, kan kudi fan miliyan 30, in ji (Telegraph).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lucas Perez

Arsenal ta sanar da Lazio cewar dole ta biya fan miliyan 7 idan tana son dan wasan gaban Sfaniya Lucas Perez mai shekara 29, in ji Corriere di Roma, .

Leicester za ta karbi fan miliyan 18 a kan dan wasan gabanta dan kasar Aljeriya, Islam Slimani, amma ta yi wu ba za ay anke shawara a kan makomar dan kwallon mai shekara 30 ba, har zuwa karshen watan Agusta,in ji (Leicester Mercury).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Adrien Rabiot

Chelsea ta sabunta kwantiragin Kante, inda ya kai fan 290,000 a ko wane mako, lamarin da zai sa ya zama dan wasan da aka fi biya a kungiyar, in ji Times - subscription required.

Dan wasan tsakiyar Paris St-Germain dan kasar Faransa, Adrien Rabiot, mai shekara 23, ya kusa sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da zakarun gasar Ligue 1, in ji ESPN.