Everton ta sayi Digne daga Barcelona

Dan wasan ya buga wasanni 46 a cikin shkaru biyu a Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan wasan ya buga wasanni 46 a cikin shekara biyu a Barcelona

Kungiyar Everton ta sanar da sayen Lucas Digne na baya-bayan nan daga Barcelona a kwantiragin shekaru biyar inda za su biya shi fam miliyan 18.

Dan wasan, mai shekara 25, ya koma Barca daga Paris St-Germain a shekarar 2016, kuma ya lashe gasar La Liga da Ligue 1 a lokacin da yake tsohuwar kungiyarsa.

Digne ya fada cewa "Everton babban kulob din kwallon kafa ne, mai tarihi mai kau. Ina so na yi wasa, na yi nasara da wasannin kuma na ja magoya baya tare da ingancin kwallon kafa."

"Ina so na yi wasan kwallon kafa mafi kyau a nan. Kowane mutum na son gasar Premier, kuma gaskiya ina jin dadin dawo wa nan barin."

"Ba na jin tsoro, ina farin ciki, a gare ni, sabon abu ne na gano a kan garin, wasanni, mutane da kuma babban kungiyar kwallon kafa kamar Everton."

Digne wanda ya shafe shekara daya a matsayin aro a Roma ya buga wasanni 46 a Barcelona.

Dan kwallon ya yi ban kwana da mutanen kungiyar da zai bari tare da gode musu kan yadda suka sa kungiyar ta zame masa kamar "gida domin ya dauke su tamkar 'yan uwansa," a cewarsa.,