Da gaske Barca na neman Pogba? Ina Courtois zai koma?

Yerry Mina Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yerry Mina

Manchester United ta shirya domin taya dan wasan bayan Barcelona dan kasar Colombia,Yerry Mina, mai shekara 23, bayan ta kasa sayen dan wasan Leicester City, mai shekara 25, Harry Maguire, in ji jaridar (Mirror).

Everton ba ta son ta biya Barcelonafan miliyan 35 kan Mina, kuma maimakon haka za ta nemi dan wasan bayan Manchester United dan kasar Argentina, Marcos Rojo, mai shekara 28, a cewar (Goal).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lewis Cook

Tottenham na kokarin taya dan wasan tsakiyar Bournemouth,mai shekara 21, Lewis Cook, wanda ya jagoranci 'yan wasan Ingila a nasarar da suka yi a gasar kofin duniya ta 'yan kasa da shekara 20 a lokacin bazarar bara kan kudi fan miliyan 30, in ji (Star).

Chelsea na fuskantar barazanar rasa dan wasan tsakiyar Belgium, mai shekara 26, Thibaut Courtois idan ba su samu wanda zai maye shi ba kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar 9 ga watan Agusta, kamar yadda jaridar (Mail)ta bayyana.

Chelsea na son dan wasan Aston Villa, mai shekara 22, Jack Grealish, wanda Tottenham ma take zawarci, in ji jaridar (Sun).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mateo Kovacic

Dan wasan tsakiyar Real Madrid da Croatia Mateo Kovacic, mai shekara 24, ba zai koma Manchester United domin ba ya son ya yi wasa a karkashin kocin Red Devils Jose Mourinho, in ji (Marca).

Adrien Rabiot, mai hskeara 23, zai iya barin Paris St-Germain idan zakarun na gasar Ligue 1 suka sayi takwaransa na Faransa N'Golo Kante, mai shkeara 27, daga Chelsea, in ji Mundo Deportivo, .

Bayer Leverkusen ta tuntubi Tottenham kan sayen dan wasan tsakiyar Ingila, mai shekara 19, Marcus Edwards, kamar yadda jaridar (Sun) ta ruwaito.

Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya shirya domin tattaunawa da dan wasan Brazil Willian, mai shekara 29, yayin da Real Madridda Manchester United da kuma Barcelona na sha'awar sayen dan wasan, in ji (Star).

Dan wasan tsakiyar Serbia Sergej Milinkovic-Savic zai ci gaba da zama a kungiyar Lazio a wannan kakar.

An alakanta dan wasan, mai shekara 23 da koma wa Manchester United da Chelsea a wannan lokacin bazarar, a cewar jaidar (Star).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paul Pogba

Daraktan horaswa na Barcelona Eric Abidal ya musanta cewa ya gana da Paul Pogba domin tattauna sayen dan wasan, mai shekara 25, da ke taka leda a Manchester United da Faransa, in ji Mundo Deportivo.

Saura kiris a kammala cinikin dan wasan gaban Argentina, Gonzalo Higuain, mai shekara 30, daga Juventus zuwa AC Milan, kamar yadda aka ambato manajan Milan, Beppe Marotta a Gazzetta dello Sport, a ESPN).

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mattia Caldara

AC Milan ta shirya domin sayen wani dan wasan da Chelsea ke nema - dan wasan bayan Juventus da Italiya Mattia Caldara, mai shekara 24 - a wata yarjejeniyar musaya da za ta hada da dan wasan bayan Italiya, mai shekara 31, Leonardo Bonucci, in ji (Mail).

Sai dai kuma, Chelsea ba ta yanke kauna ba kan sayen Higuain, kuma za su iya sayar da dan wasan gaban Faransa, mai shekara 31, Olivier Giroud ga Marseille domin samun kudin yarjejeniyar, a cewar(Mirror).

Labarai masu alaka