Ya ake ciki da cinikin Modric, Mina, Vidal, Courtois da Lewandowski?

Yerry Mina Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid ta ce tana son fam miliyan 670 kan dan wasan tsakiyar Croatia mai shekara 32, Luka Modric, wanda ya zama gwarzon dan wasa na gasar kofin duniya ta 2018, domin ta hana Inter Milan taya dan wasan, in ji Mirror.

Manchester United ta cimma yarjejeniya da dan wasan bayan Barcelona mai shekara 23, Yerry Mina, yayin da da dan wasan na Colombia yake dakon kungiyoyin su cimma matsaya, in ji Mundo Deportivo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 25, ya shaida wa takwarorinsa na kulob din cewar ya shirya domin barin Crystal Palace kuma zai iya mika takardar da za ta tilasta ya koma Chelsea, in ji Mirror.

Barcelona ta cimma matsaya da dan wasan Bayern Munich Arturo Vidal, inda dan wasan Chile din mai shekara 31 zai sa zakarun Sfaniya din su kashe fam miliyan 27, in ji Guardian.

Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya shirya domin fara tattaunawa da gola Thibaut Courtois, yayin da Real Madrid take shaukin sayen dan wasan Belgium din mai shekara 26, in ji Diario AS.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amma the Blues sun yi watsi da tayin fan miliyan 31 da Madrid ta yi wa Courtois, tana ganin cewa tayin ya yi kadan, in ji Express.

Chelsea tana son dan wasan Real Madrid Mateo Kovacic bayan rahotanni sun ce dan wasan Croatia din mai shekara 24 ya ki komawa Manchester United don irin salon wasan Jose Mourinho, in ji Calciomercato - in Italian.

Dan wasan bayan Chelsea da Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 22, zai nemi koma buga wasan aro a ketare idan bai samu isasshen lokacin wasa ba da farkon kaka, in ji Times - subscription required.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Toby Alderweireld

Dan wasan bayan Belgium, Toby Alderweireld, mai shekara 29, ya shirya domin katse yarjejeniyarsa da Tottenham idan ya kasa komawa Manchester United kafin lokacin da za a rufe kasuwar musayar 'yan wasa a mako mai zuwa, in ji Mirror.

Everton na fuskantar gogayya wajen sayen dan wasan bayan Manchester United Marcos Rojo yayin da Paris St-Germain daMarseille da kumaZenit St Petersburg ke son dan wasan mai shekara 28, in ji Sun.

Manchester United tana tunanin bayar da dan wasan gaban Faransa Anthony Martial, mai shekara 22, ga Bayern Munich a matsayin wata yarjejeniya ta sayen dan wasan gaban Poland Robert Lewandowski, mai shekara 29, in ji Mirror.

Duk da haka, rahotanni a Jamus na cewa maimakon haka za a yi amfani da Martial ne wajen musayar dan wasan bayan kungiyar ta gasar Bundesliga mai shekara 29, Jerome Boateng, in ji Bild.

Labarai masu alaka