'Man Utd ko Liverpool ko Arsenal ne kawai za su raba Gerrard da Rangers' - Miller

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Gerrard's man-management crucial - Adam

Steven Gerrard ba zai bar kungiyar Rangers ba sai idan Liverpool ko Manchester United ko Arsenal ne suka bukaci ya zama kocinsu.

Wannan maganar ta fito ne daga bakin Alex Miller, wani tsohon mataimakin mai horas da kungiyar Liverpool a lokacin da Steven Gerrard ke taka leda a kungiyar.

Mista Miller ya taba buga ma kungiyar Rangers lokacin yana matashi.

Ya kuma ce yana da karfin gwuiwa cewa Rangers za ta sami daukaka a karkashin sabon koci Steven Gerrard.

Ya fada ma BBC Scotland cewa: "Rangers za su ja daga da kungiyar Celtic nan ba da jimawa ba".

Ya kara da cewa, "Idan ka sami aikin horas da Rangers, me zai sa ka tafi? Sai dai idan kungiyoyi kamar Liverpool ko Manchester United ko kuma Arsenal ne suka bukaci ka zama kocinsu."

Miller na ganin cewa 'yan wasan da Gerrard ya saya a kakar wasa na bana zasu yi tasiri a gasar firimiyar Scotland.

Kawo yanzu, Rangers sun sai 'yan wasa 10, kuma sun bambanta da irin 'yan wasan da aka saba gani a kungiyar ta Ibrox.

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Gerrard yayi wasa karkashin jagorancin Alex Miller da Rafa Benitez a kungiyar Liverpool

Miller ya taba zama mataimakin kocin Scotland a karkashin Craig Brown kafin daga baya ya rike irin wannan mukamin a karkashin Rafa Benitez a Liverpool, kuma ya horas da Steven Gerrard na wasu shekaru.

Labarai masu alaka