Chelsea na zawarcin Zaha, Everton na neman Mina

Yerry Mina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yerry Mina

Kungiyar Everton ta cimma yarjejeniya da Barcelona kan dan wasan Colombia Yerry Mina, mai shekara 23, a kan fam miliyan 28.5, in ji (Sport - in Spanish).

Everton ta sanar wa Manchester United cewa za ta karbi dan wasan Ingila Chris Smalling, mai shekaru 28, ko dan wasan bayan Sweden Victor Lindelof, mai shekara 24, idan kolub din biyu suka kasa cimma yarjejeniya game da dan kwallon Argentina, Marcos Rojo, kamar yadda (Teamtalk) ta bayyana.

Manchester United na shirye-shirye don neman dan wasan Leicester, Harry Maguire, mai shekara 25, kuma sun san cewa za su biya makuddan kudi domin karbar dan wasan na Ingila, kamar yadda (Sky Sports) ta ruwaito.

A halin yanzu, Manchester United ta tuntubi Bayern Munich don sayar da dan wasan Jamus, Jerome Boateng, mai shekara 29, wanda aka kimanta a kan fam miliyan 44, kamar yadda (Bild - in German) ta ruwaito.

Chelsea na da sha'awar sayen Wilfried Zaha, na Crystal Palace da dan Ivory Coast, mai shekara 25, bayan Tottenham ta fita daga zawarcinsa, in ji jaridar (Mirror).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wilfried Zaha

Kocin Chelsea Maurizio Sarri ya ba da shawara cewa Thibaut Courtois, mai shekara 26, wanda yake Real Madrid za a sayar da shi idan ya so barin kungiyar, kamar yadda jaridar (Times) ta ce.

Saura shekara daya kwantaragin dan wasan Arsenal, Aaron Ramsey, ta kare a kungiyar, kuma wakilansa sun musanta cewa dan wasan, mai shekara 27, ya nemi a biya shi fam 300,000 a kowane mako a wata sabuwar yarjejeniya, a cewar jaridar (Express).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Stanislav Lobotka

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino yana sha'awar dan wasan tsakiya na Celta Vigo, Stanislav Lobotka, wanda ke da albashin fam miliyan 31 a kwangilarsa, kamar yadda jaridar (Mirror) ta ruwaito.

Kungiyar Leicester City tayi tayin dan wasan kungiyar Brentford, Chris Mepham, mai shekara 20, a kan fam miliyan 10 amma kungiyar ba ta amince ba, kuma Bournemouth su ma suna so su sayi dan wasan na Wales, a cewar jaridar (Mail).

Wolves suna son su biyan Middlesbrough fam miliyan 22 a kashi-kashi don siyan dan wasan Spain Adama Traore, mai shekara 22 a kan su biya su fam miliyan 18 a nan take, in ji jaridar (Sun).

Crystal Palace tana fara tattaunawa a kan yarjejeniyar sayan dan wasan kasar Israel, Munas Dabbur, mai shekara 26,a cewar jaridar (Mail).