Dole Bukola Saraki ya bar majalisa —Akpabio

Godswill Akpabio Hakkin mallakar hoto Facebook/ Godswill Akpabio

Tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom, Sanata Godswill Akpabio, ya ce dole shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya bar majalisar idan ana so a kori shi Akpabio daga majalisar.

Sanata Akpabio, wanda ya bar mukaminsa na shugaban marasa rinjaye a majalisar a lokacin da ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC, ya fadi wannan maganar ce a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

Saraki ya bi sawun wasu sanatoci da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mara rinjaye lamarin da ya sa jam'iyyar APC mai rinjaye ke cewa ya kamata ya sauka daga shugabancin majalisar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato Akpabio yana cewar idan wasu suna neman a ayyana cewar babu kowa kujerar mazabarsa a majalisar saboda ya koma APC, dole Saraki da wadanda suka bar APC su ma su bar kujerunsu a majalisar.

Akpabio ya ce "duk wanda ya bar APC zuwa PDP, za mu ayyana kujerarsa a matsayin kujerar da babu kowa."

Cikin 'yan kwanakin nan dai an yi guguwar sauya sheka a siyasar Najeriya kamar yadda a aka yi gabannin zabukan 2015.

Hakkin mallakar hoto Facebook/Bukola Saraki

Yayin da wasu ke ganin guguwar sauya shekar za ta iya tasiri kan yunkurin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na sake komawa kan karagar mulki a shekarar 2019, wasu gani suke sauye-sauyen shekar ba za ta hana Buhari komawa wa'adi na biyu ba.

Labarai masu alaka