Ronaldo, Modric da Salah na takarar gwarzon dan kwallon Fifa

Cristiano Ronaldo, Luka Modric and Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Cristiano Ronaldo, da Luka Modric da Mohamed Salah sun tsallake zuwa matakin karshe na zaben gwarzon dan kwallo kafar duniya na Fifa na 2018.

Dan wasan gaba na Barcelona da Argentina Lionel Messi, wanda kuma sau biyar yana lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniya ta Ballon d'Or winner, ba ya cikin mutum uku na karshe da ke takarar.

Kazalika babu wani dan wasan kasar Faansa, wacce ta dauki kofin duniya na bana, da ke cikin masu fafatawa domin zama gwarzon dan kwallon kafar duniya na bana.

'Yan wasan Lyon biyu Ada Hegerberg ta kasar Norway da 'yar kasar Jamus Dzsenifer Marozsan da 'yar kasar Brazil Marta ne suka kai mataki ukun karshe na gwarzuwar 'yar kwallon kafar Fifa a rukunin mata.

Dan wasan Portugal Ronaldo, wanda ya lashe kyautar a 2016 da 2017, ya dauki kofin zakarun turai karo na biyar a watan Mayu, lokacin yana wasa da Real Madrid kafin ya koma Juventus a kan £99.2m.

Dan wasan tsakiya na Real Madrid Luka Modric ne ya samu kyautar dan kwallon kafar duniya na 2018 bayan kasarsa Croatia ta kai matakin karshe na gasar inda ta fafata da Faransa.

Dan wasan gaba na Masar Salah ya ci kwallo 44 a Liverpool inda kulob din ya kai zagayen karshe na gasar zakarun turai, ko da yake ya sha kashi a hannun Real.

Modric ya doke Ronaldo da Salah inda ya zama gwarzon dan kwallon kafar Uefa na bana.