Dole Leroy Sane ya kara kokari, in Toni Kroos

Joachim Low da Leroy Sane

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sane na daga yan wasan da suka ttaimakawa Manchester City ta lashe kofin premier a kakar da ta gabata, amma bai bugawa Jamus ba a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha.

Dan wasan Jamus Toni Kroos ya ce Leroy Sane ba ya taka leda kamar yadda ya kamata, kuma dole ya kara matsa kaimi wajen gyara yadda yake taka leda kamar yadda takwaran wasansa a tawagar kwallon kafar Jamus ke yi.

Sane, mai shekara 22, bai samu shiga cikin 'yan wasan da suka buga wa Jamus gasar kofin duniya ba ,amma ya koma cikin tawagar Jamus din don buga wasan kasashen Turai inda kasarsa za ta kara da Faransa ranar Alhamis, da kuma wani wasan sada zumunci da Peru.

Amma tun da aka fara kakar bana City ba ta fara wasa da shi ba, kuma bai buga wa kungiyar ba ranar Asabar.

"A wasu lokuta za ji kamar Leroy bai damu ba ko mun ci ko ba mu ci ba," in ji Kroos .

"Dan wasa ne da yake da komai da kake bukata wajen kasacewa gwarzon dan wasa a duniya, amma a wasu lokuta dole ka gaya masa cewar yana bukatar kara matsa kaimi," kamar yadda dan wasan tsakiyar Real Madrid din mai shekara 28 ya bayyana.

Sane ya ci kyautar kungiyar 'yan wasa ta matashin da ya fi iya taka leda a kakar 2017-18 inda ya ci kwallo 10 kuma ya taimaka aka ci kwallo 15 a gasar Firimiya.

Amma wasan minti 30 kawai ya buga wa City a wannan kakar.