Paul Pogba: Ba tabbas kan ci gaba da zamana a United

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pogba ne ya yi wa Man U kyaftin a wasannin farko na Gasar Firimiyar bana

Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya ce har yanzu yana kungiyar sai dai ya ce ba shi da tabbacin ci gaba da kasancewa da kungiyar na tsawon lokaci.

A kakar bara ce aka alakanta dan wasan mai shekara 25 da komawa kungiyar Barcelona.

A watan jiya ne kocin kungiyar Jose Mourinho ya ce "ba ya farin ciki" da Pogba.

Dan kwallon wanda ya lashe Kofin Duniya ya shaida wa kafar yada labarai ta Sky Germany cewa: "Makomata tana Manchester."

"Ina da sauran kwantiragi a kungiyar, ina yin wasa a can, amma waye ya san abin da zai faru nan da 'yan watanni."

Mourinho ya ajiye Pogba a benci a wasanni biyun da kungiyar ta buga da Sevilla.

Sai dai shi ne ya yi wa kungiyar kyaftin a wasannin farko da suka buga a firimiyar bana, kuma ya yi nasarar zura kwallaye biyu a raga kawo yanzu.

A wata hira da manema labarai dan wasan ya ce yana da "dangantaka mai kyau tsakaninsa da kocinsa."