Dan wasan Madrid Marcelo ya ki biyan haraji a Spain

Marcelo Vieira Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Real Madrid Marcelo Vieira ya amince cewa ya zille wa biyan haraji inda ya yarda a yi masa daurin je-ka-ka-gyara-halinka na wata hudu, in ji kafofin watsa labaran Spain.

Rahotanni sun ce dan wasan dan kasar Brazil mai shekara 30 ya ha'inci hukumomin Spain $576,000 ta hanyar yin amfani da kamfanonin kasashen waje wurin tafiyar da harkokin kudinsa.

Kazalika zai biya tarar €750,000.

Yana daya daga cikin 'yan wasan kwallon kafa da hukumomin karbar haraji suka hukunta.

Marcelo ya amince cewa ya kauce wa biyan haraji kuma an rage masa daurin da ya kamata a yi masa ne da ma tarar da ya kamata ya biya a wani bangare na yarjejniyar da ya kulla da masu shigar da kara, a cewar rahoton da El Mundo da EFE suka bayar.

Dokokin Spain sun amince wanda ya aikata laifi karon farko ya sha daurin je-ka-ka-gyara-halinka na shekara biyu, don haka ana sa ran ba zai yi zaman gidan yari ba.

An zargi 'yan wasan kwallo kafa da dama da kauce wa biyan haraji, cikin su har Lionel Messi, Neymar da Cristiano Ronaldo.

Labarai masu alaka