Ko kun san abin Diego Maradona yake yi?

Saura kuma sun yi babban hoton gwarzon kwallon kafar ne. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saura kuma sun yi babban hoton gwarzon kwallon kafar ne.

Gwarzon dan kwallon Argentine Diego Maradona ya ce sabon aikinsa na koci a wata kungiyar kwallon kafa ta kasar Mexico tamkar sabuwar rayuwa ce gare shi, bayan shekarun da ya shafe yana fama da matsalar ta'ammali da kwaya da shan barasa da kuma teba.

Sai dai kuma wasu sun yi mamakin zabin da ya yi na kungiyar Dorados a jihar Sinaloa, wanda gida ne ga daya daga cikin manyan masu fataucin miyagun kwayoyi a kasar Mexico.

Ya ce aikin dake gabansa a Dorados zai yi kama da "daukar giwa a kafadunmu."

A halin yanzu kulob din yana mataki na 13 a gasar 'yan rukuni na biyu na kasar Mexico, wadda ake ce wa Liga Ascenso.

Kungiyar ba ta samu nasara ko sau daya ba a wasanninta shida na farko.

Duk da haka, Maradona ya ce zai yi aikin koci ta hanyar mayar da hankali kan kai hare-hare, kamar yadda ya taka leda a lokacin da yake wasa.

A taron manema labaransa na farko, Maradona ya ce: "Za mu yi kokarin yin nasara a wasanni don ba na son in yi wasa ina tsare gida."

Ya kuma yi bayani game da matsalolin da ya fuskanta a baya. "Na yi kurakurai da yawa a rayuwata. Na dauki alhakin wadannan kamar wanda ya rike yaro a hannayensa," in ji shi.

"A lokacin da nake shan [kwaya] ... lamarin ya sa na yi baya, komabaya ne, kuma abin da ya kamata 'yan wasan kwallon kafa su yi shi ne su nemi cigaba."

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An bai wa Maradona rigar kwallon Dorados, da ke dauke da lambar da yake sakawa a lokacin da yake taka leda.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan ne aikin koci na baya bayan nan na dan kasar Argentina.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Maradona ya yi fama da teba da kuma matsalar ta'ammuli da miyagun kwayoyi a cikin 'yan shekarun nan
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maradona ya bayyana aikinsa a Dorados a matsayin wani "sabon abu"

A baya dai tsohon dan wasan Barcelona da Napoli din ya yi aikin koci a kungiyoyin hadaddiyar daular Larabawa Al-Fujairah da kuma Al-Wasl, kuma ya yi aikin kocin tawagar kwallon kafar Argentina daga shekarar 2008 zuwa 2010.

"Na zo nan ne in yi aiki . Na zo nan ne in zage dantse kamar yadda na yi a Fujairah, inda na yi ta tukin kilomita 300 zuwa aiki a ko wace rana ," in ji Maradona .

Duk da cewa kafafan watsa labarai na cikin gida sun bayar da rahoton cewar mazauna unguwar da Maradona ke fatan zama sun dakile yunkurin, yawancin masoya Dorados sun ba da goyon baya.

"Mun yarda da kai, Diego. A nan ba ma suka, kauna kawai muke yi," in ji wata alama da wani masoyin kulob din ya dauka.

A kasar Mexico ne Maradona ya fi taka rawar gani a tamaula a matsayinsa na dan wasa a lokacin da ya jagoranci kasarsa wajen cin kofin duniya a shekarar 1986.

Amma ya ce shi bai zo kulob din ba domin tuna baya. "Ba mu zo nan ba domin yawo, ba mu zo nan yawon buda ido ba, mun zo aiki ne... zai yi kyau mu yi nasara tare, zai yi kyau mu yi nasara tare," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daruruwan magoya bayan Dorados sun fito domin kallon atisayen Maradona na farko
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sun marabci Maradona zuwa kulob dinsu da kyallaye masu rubutu.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saura kuma sun yi babban hoton gwarzon kwallon kafar ne.

Labarai masu alaka