Ina arsene Wenger yake ne?

Arsene Wenger yana shakatawa da 'yan uwa da abokan arziki a watan Yuni Hakkin mallakar hoto ZSOFI ZSARNAI
Image caption Arsene Wenger yana shakatawa da 'yan uwa da abokan arziki a watan Yuni

A cikin watan Mayu ne dai Arsene Wenger ya ajiye aikinsa na kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal bayan ya shafe shekara 22 yana jagorantar kungiyar.

Bayan kocin mai shekara 69 ya bar kungiyar Arsenal wadda ta sa ya yi fice a watan Mayun shekarar 2018, an yi ta rade-radi game da makomar kocin.

Zai koma wani kulob aiki ne ko kuma zai hakura da aikin horaswa?

Rahotanni dai sun nuna cewa tsohon kocin Arsenal din yana amfani da damar hutun da ya samu wajen shakatawa.

Image caption Wasu daga ciki shahararun 'yan wasan da suka yi tamaula a Arsenal karkashin jagorancin Wenger

A cikin watan Yuni an ga Wenger ya shiga kwale-kwale da 'yan uwa da abokan arziki a Cambridge.

Sai dai kuma duk da cewa mutane sun nemi daukar hoto da shi, Wenger bai nuna damuwa ba.

Abin da ya dame shi kawai shi ne yadda mai tuka jirgin kwale-kwalen ba zai fadi ba.

A lokacin da ake gasar kofin duniya, daga watan Yuni zuwa watan Yuli, Wenger ya yi aiki a matsayin mai fashin baki ka wasanni ga kafar beIN Sports.

A hirar da ya yi da wasu kafafan yada labari Wenger ya nuna cewa ba zai sauya sana'a ba. sai dai kuma bai nuna inda zai koma ba.

Amma bayan shakatawa da karance-karance, Wenger yana yawo kasashen duniya musamman Yammacin Afrika.

Hakkin mallakar hoto ZSOFI ZSARNAI

Ranar 24 ga watan Augusta ne tsohon dan wasan Wenger George Weah wanda a yanzu shgaban kasar Laberiya ne ya karrama shi da lamabar yabo mafi girma a kasar.

A ranar ne kuma tsohon shugaban kasar Ghana, John Agyekun Kufor, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar, dan kasar Faransan ya ziyarce shi.

Fitattun 'yan wasan da suka bar Wenger a Arsenal

 • Jens Lehmann: Ya bar Arsenal a 2008 ya koma Stuttgart lokacin da kwantiraginsa ya kare a kungiyar daga baya ya yi ritaya. Ya sake komawa tamaula a 2011 daga nan ya sake shiga Arsenal.
 • Bacary Sagna: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Landan.
 • Kolo Toure: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Arsenal.
 • Thomas Vermaelen: A shekarar 2014 ya koma Barcelona.
 • Ashley Cole: Ya koma murza-leda a Stamford Bridge ita kuwa Chelsea ta bayar da William Gallas.
 • Patrick Vieira: Ya koma wasa ne a Juventus.
 • Cesc Fabregas: A shekarar 2003 ya koma murza-leda a Barcelona.
 • Marc Overmars: A shekarar 1997 ya koma Barcelona domin maye gurbin Luis Figo.
 • Alexis Sanchez: Ya koma Old Trafford, inda Manchester United ta bayar da Henrikh Mkhitaryan.
 • Robin van Persie: A shekarar 2012 ya koma murza-leda a Manchester United.
 • Thierry Henry: Ya koma buga tamaula a Barcelona a 2000.

Labarai masu alaka