'Yan PDP sun yi zanga-zanga a Abuja

PDP Hakkin mallakar hoto Twitter @Bukola Saraki
Image caption Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Shugaban jam'iyyar PDP Uche Secondus ne suka jagoranci zanga-zangar

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi zargin cewa Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi musu murdiya a zaben jihar Osun.

Babbar jam'iyyar adawar ta zargi mulkin Shugaba Buhari da son bata demokaradiyyar kasa.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya ce sun fito zanga-zangar ne don su kai koken su ga ofishin hukumar zabe ta kasa (INEC) da kuma hedikwatar rundunanr 'yan sandan kasar.

Mista Ologbondiyan ya shaida wa BBC cewa suna zanga-zangar ne kan yadda hukumar INEC ta gudanar da zaben jihar Osun da ke kudu maso yammacin kasar.

Jam'iyyar PDP dai na zargin jam'iyyar APC mai mulki da yin magudi a zaben. Sai dai jam'iyyar ta musanta zargin.

Hakkin mallakar hoto Twitter @Bukola Saraki
Image caption Sai dai 'yan sanda sun harba wa masu zanga-zangar hayaki mai sa hawaye yayin da suka isa hedikwatar rundunarsu

Dan takarar jam'iyyar APC, Gboyega Oyetola ne ya ci zaben jihar Osun bayan da aka karasa shi a makon jiya.

A zaben farko da a ka yi dai, Ademola Adeleke wanda a ka fi sani da "sanata mai rawa" na jam'iyyar PDP ne ya ci.

Amma hukumar zabe ba ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba.

Mista Ologbondiyan ya ce gwamnatin tarayya da jam'iyyar APC na son bata dimokaradiyyar Najeriya.

Hakkin mallakar hoto Twitter @BukolaSaraki

Ya ce jam'iyyar PDP na son gwamnati ta bar INEC ta yi aikinta ba tare da sa bakin gwamnatin ba.

Ya ce hukumar zaben na aiki ne kamar wata hukumar gwamnati.

Hakkin mallakar hoto Twitter @BukolaSaraki