Ana kame kan cuwa-cuwar sayen 'yan wasa a Turai

Kociyan Club Bruges Ivan Leko Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kociyan Club Bruges na Belgium Ivan Leko yana daga cikin wadanda 'yan sanda ke bincike

An yi wa wasu jami'an manyan kungiyoyin kwallon kafa na Belgium dirar-mikiya a wani bincike da 'yan sanda ke yi na zargin cin-hanci da zamba a cinikin 'yan wasa.

Kafofin watsa labarai na kasar ta Belgium sun ruwaito cewa binciken ya hada da wakilan 'yan wasa da alkalan wasa da kuma jami'ai daga manyan kungiyoyi wadanda suka hada da Anderlecht da Club Bruges da kuma Standard Liege.

Ana yi wa kociyan kungiyar Club Bruges Ivan Leko da kuma fitaccen eja din nan dan kasar Belgium da kuma Iran Mogi Bayat tambayoyi dangane da badakalar.

'Yan sanda sama da 200 ne suke cikin aikin binciken a kasashe da dama.

Masu gabatar da kara sun kuma ce 'yan sanda sun yi dirar-mikiya a wurare a Faransa da Luxemburg da Cyprus da Montenegro da kuma Serbia da Macedonia.

Sanarwar ta ce a yanzu mutane da yawa na fuskantar tambayoyi.

Kungiyar Club Bruges wadda take kokarin ganin ta ci gaba da rike matsayinta a gasar Zakarun Turai bayan ta sha kashi 3-1 a hannun Atletico Madrid a makon da ya wuce, ta tabbatar da cewa 'yan sanda sun yi wa kociyan nata tambayoyi.

Shi kuwa Mista Bayat rahotanni sun ce a rana Laraba ne aka kama shi a gidansa. Ana ganin cewa eja din yana daya daga cikin wadanda aka fi hari kan binciken da ake yi na zamba da kuma kokarin halatta kudaden haram.

Binciken wanda aka fara a shekarar da ta wuce zai mayar da hankali ne a kan zargin almundahana a cinikayyar 'yan wasa a kakar 2017-2018 a Belgium in ji kafar watsa labarai ta VRT ta kasar.

Labarai masu alaka