An sace kofin gasar Faransa

Zakarun gasar wannan shekarar ta tseren keke ta Faransa,Tour de France, Geraint Thomas na daya a tsakiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zakaran fitacciyar gasar tseren keke a duniya ta Faransa, Tour de France, Geraint Thomas rike da kofin da aka sace a tsakiya

Zakaran fitacciyar gasar tseren keke ta duniya ta Faransa wadda ake kira Tour de France da Faransanci, Geraint Thomas ya roki barayin da suka sace kofin da aka ba shi da su dawo da shi.

A yanzu dai 'yan sanda sun dukufa bincike kan sace kofin wanda ake bayar da shi duk shekara, yayin wani bikin kalun-kowa na kekuna.

An sace kofin ne wanda da Faransanci ake kira Coupe Omnisports bayan da kungiyar Thomas wato Team Sky ta bayar da aronsa ga masu shirya kallun-kowar na keke a Birmingham.

Mista Thomas ya ce kofin yana da matukar muhimmanci a wurinsa da kuma kungiyarsa.

An ba wa zakaran dan yankin Wales kofin ne mai launin baki da ruwan zinariya, kuma kirar hannu, a bazarar nan lokacin da ya zama dan Birtaniya na uku da ya taba cin gasar ta tseren keke ta Faransa.

An dauke kofin ne wanda aka dora a kan tebur lokacin bikin da kamfanin Italiya da ya kera kekunan kungiyar Team Sky ta Thomas, Pinarello.

A daidai lokacin da aka bar kofin ba tare da kowa ba lokacin da ake tashi daga bikin ne sai aka sace shi.