Real Madrid ta kafa mummunan tarihi

Kociyan Real Madrid Julen Lopetegui

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lopetegui tsohon golan Barcelona da Real Madrid yana cikin matsi kan halin da Madrid din ke ciki a yanzu

Real Madrid ta kafa mummunan tarihi bayan da ta yi rashin nasara karo na hudu a wasa biyar, bayan da Levante ta doke ta a Bernabeu da ci 2-1.

Sakamakon ya kara jefa kociyanta Julen Lopetegui cikin matsi, inda kungiyar ta ci gaba da zama ta biyar a teburin La Liga, da bambancin maki uku a bayan ta daya Alaves mai maki 17 a wasa 9.

Sau biyu aka daga ragar Real Madrid a cikin minti 13, inda da farko a minti na 6 Morales ya fara ci, sannan kuma a minti na 13 Marti ya ci ta biyu da fanareti.

'Yan wasan Real sun yi ta kai hare-hare masu kyau bal din na bugar karfen raga, a wasu lokutan kuma golan bakin Oier Olazabal ya kade ko ya kama.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Marco Asensio ya daga raga a kashin farko na wasan, amma aka hana da cewa ya yi satar gida

A minti na 72 ne Marcelo ya kwararo wata bal ta yi wa mai tsaron ragar Levanten gaya-wa-jini-na-wuce ta kwana a ragarsa.

Kafin wasan na Asabar daraktan Real Madrid Emilio Butragueno ya nuna goyon bayansa ga kociya Lopetegui, to amma yadda suke fuskantar muhimmin wasa na gasar Zakarun Turai a gabansu, da kuma wasan hamayya da Barcelona, El Clasico a karshen mako na gaba, shugabannin kungiyar za su sha matsin lamba kan su hanzarta daukar mataki.

Sakamakon sauran wasannin na La Liga na Asabar

Valencia 1-1 Leganes

Villareal 1-1 Atletico Madrid