Real Madrid ta kori kocinta Julen Lopetegui

Julen Lopetegui

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Lopetegui ya lashe wasanni biyar, ya fadi biyar, ya yi kunne doki biyu a wasanni 12 da ya jagoranci Real Madrid

Kungiyar Real Madrid ta kori Julen Lopetegui daga mukaminsa na kocin kungiyar bayan wata hudu da rabi yana jan ragamar kungiyar daga Bernabeu.

Kocin ya gaji Zinedine Zidane a watan Yunin da ya gabata ne.

Kungiyar ta sha kaye a hannun Barcelona a wasan El Clasico na Lahadi, wanda shi ne rashin sa'a a wasanni biyar cikin shida da ta buga a jere.

A sabili da haka Real na mataki na tara a kakar wasan La Liga na bana bayan da suka lashe gasar Zakarun Turai a jere shekaru uku da suka gabata.

Wannan ce kakar wasa mafi koma baya da suka taba fuskanta tun shekarun 2001-2002.

An nada Santiago Solari, tsohon dan wasan kungiyar mai shekara 42 ya rike kungiyar na wucin gadi kafin a nada sabon koci.

Solari ne kocin kungiyar Real Madrid ta biyu, wato Team B a halin yanzu.

Lopetagui ya horas da 'yan wasan kungiyar a yau Litinin, amma an sallame shi ne jim kadan bayan masu kungiyar sun tashi daga wata ganawa ta gaggawa da suka yi.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce "Akwai wani gagarumin gibi tsakanin kwarewar da Real Madrid ke da shi ta 'yan wasa" idan aka kwatanta da "sakamakon da ake samu a 'yan kwanakin nan."

Ana ganin Real za ta nada tsohon kocin Chelsea, Antonio Conte ya gaji Lopetegui.

Chelsea ta kori Antonio Conte a watan Yuli, kuma tun lokacin bai sami aikin horas da wata kungiya ba.