Dele Alli ya sabunta kwantaraginsa a Tottenham

Dele Alli playing against Man City on Monday

Asalin hoton, AFP

Dan wasan tsakiya na Tottenham Dele Alli ya sanya hannu a sabon kwantaragi lamarin da zai sa ya ci gaba da zama a kulob din har shekarar 2024.

Dan wasan mai shekara 22 ya komaTottenham a kan joined Spurs for £5m a 2015, kuma ya zura kwallo 48 a wasa 153 da ya buga wa kulob din.

Ya buga wasa shida a gasar Firimiya ta bana - ciki har da kayen da suka sha a hannun Manchester City ranar Litinin a Wembley - ko da yake ba zura kwallo ba tun da aka soma gasar.

Ya koma kulob din ne daga kulob din matasa MK Dons inda ya soma wasa yana da shekara 16 a duniya.

Alli ya bi sahun takwarorinsa na kulob din irin su Harry Kane da Son Heung-min da kuma Harry Winks wajen sanya hannu a sabon kwantaragin.