Qatar 2022: Kasashe 48 ne za su je gasar cin kofin duniya

Asalin hoton, Getty Images
Gianni Infantino ya fara shugabancin hukumar Fifa ne a watan Fabrairun shekarar 2016
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Gianni Infantino ya ce kasashe 48 ne za su halarci gasar cin kofin duniya wacce za a yi a kasar Qatar a shekarar 2022.
A baya an shirya fara amfani da tsarin kasashe 48 ne a shekarar 2026, inda kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karbi bakuncin gasar.
Kasashe 32 ne suka halarci gasar ta bana wadda aka yi a kasar Rasha.
Sai dai wannan sauyin zai tilasta wa Qatar ta hada gwiwa da wasu kasashe a yankin Gabas ta Tsakiya don karbar bakuncin gasar, a cewar shugaban hukumar.
"Idan abu ne da zai yi wu, to me ye zai hana mu?" in ji shi.
"Muna duba yiwuwar hakan, muna tattaunawa da abokanmu a Qatar da sauran kawayenmu da ke yankin kuma muna fatan hakan mai yiwuwa ne."
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a babban taron hukumar kwallo kafa ta nahiyar Asiya a sabuwar hedkwatar hukumar a birnin Kuala Lumpur a kasar Malaysia.
"Ina so a kara bai wa kowace kasa damar fafatawa a gasar," in ji shi.