Rio Ferdinand zai auri Kate Wright

Kate Wright and Rio Ferdinand

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon dan wasan kwallon kafa Rio Ferdinand da budurwarsa Kate Wright sun sanar da cewa za su yi aure.

Masoyan sun shafe kusan shekara biyu suna nema, kuma sun sanar da labarin auren nasu ne ta shafin Instagram.

"Wannan batu ne mai faranta rai matuka... me zai hana ni amincewa da wannan auren?", in ji Kate mai shekara 27 da haihuwa, wadda ta nuna wani hoto tare da Rio da 'ya'yansa uku.

Matar Rio, Rebecca Ellison ta mutu ne a shekarar 2015 bayan ta yi fama da cutar daji.

A watan Agusta, Kate ta bayyana cewa yayin da suka fara ganin juna da Rio, mai shekara 39 da haihuwa, sai suka fara kaunar juna nan take.

Ta kuma ce ta san matar Rio ta mutu, kuma yana da 'ya'ya uku, amma ta ce "batun bai ja hankalinta ba".

"Nan take na fara son Rio, kuma daga baya da na ga 'ya'yan nasa, sai na ga su ma ina kaunarsu," kamar yadda ta ce.

A wata hira da jaridar Times da ta yi da Rio a farkon shekarar nan, Rio ya ce dangantakarsa da Kate na samun karbuwa wajen 'ya'yansa.

Ya ce, "Dangantaka ta da Kate ya taimaka wa 'ya'yana saboda akwai mace a gidan yanzu."

"A wasu lokutan su kan kyale ni su je wurinta idan suka gan ta."

Tsohuwar matarsa Rebecca na da shekara 34 a lokacin da ta mutu sanadiyyar cutar kansa a watan mayun shekarar 2015.