Usain Bolt: Mun kasa cimma matsaya da kungiyar Mariners ta Ostreliya

Bayanan bidiyo,

Bidiyo: Kalli wasan gwajin da Usain Bolt yayi da Mariners

Kokarin samun gurbin buga wasan kwallon kafa da Usain Bolt ke yi da kungiyar Central Coast Mariners ta Ostreliya ya zo karshe.

A watan Agusta ne dan kasar Jamekan mai shekara 32 ya fara wasannin gwaji da kungiyar da ke rukunin A-League na kasar.

Ya zura kwallo biyu a karon farko da ya buga wa kungiyar, a lokacin wani wasan kulla zumunta da Mariners ta yi, amma bai buga wasa ko daya ba da aka bude kakar wasa ta bana.

Kungiyar ta Mariners ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta ke cewa ba a cimma daidaito wajen kulla "yarjejeniya ta kudi" da za a biya dan wasan ba.

A watan jiya kungiyar ta ce ta yi masa tayin kwantairagi mai fanni biyu, daya na kwallon kafa, daya kuma na tallace-tallace. Amma sai wani kamfani na daban ya amince.

Kungiyar ta ce an yi ta kokarin samo wasu kamfanonin da za su amince, amma daga baya komai ya watse saboda babu alamar ci gaba.

Mamallakin kungiyar ta Mariners Mike Charlesworth ya gode wa Bolt domin zaman gwaji da yayi da kungiyar na mako takwas.

Ya kuma bayyana kokarin a matsayin wata babbar nasara.

Zakaran tseren mita 100 da mita 200 mai rike da kambun dan wasa mafi saurin gudu a duniya ya bayyana cewa babu abin da yake so a duniya kamar ya buga wa wata kungiyar kwallon kafa.

Ya gode wa kungiyar "ta Central Coast Mariners tare da ma'aikatanta da mamallakanta da 'yan wasanta da kuma masu goyon bayanta saboda irin yadda suka karbe ni a lokacin da nake tare da su."

Usain Bolt ya taba buga wasannin gwaji da wasu kungiyoyin da suka hada da Borussia Dortmund da Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu da kungiyar Stromsgodset ta kasar Norway.