Paul Pogba: Man Utd da Juventus duka gida a wurina

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pogba ya ci wa Juventus kwallaye 34 a wasanni 178

Dan wasan Manchester United Paul Pogba ya ce babu wani bambanci a wurinsa tsakanin United da Juventus.

A ranar Laraba ne Juventus za ta karbi bakuncin United a Gasar Zakarun Turai wasan rukunin H.

A watan jiya ne Juventus ta doke United a gida da ci 1-0 a wasan farko da suka buga a gasar.

Pogba ya koma United ne daga Juventus a shekarar 2016 a kan fam miliyan 89, a matsayin dan kwallon da ya fi tsada a shekarar.

Ya ce rukunin H yana da "tsauri da sosa rai musammam ma a gareni".

"Komawa ta na yi wasa a gidan Juventus wani abu ne da nake son gani," in ji Pogba.

"Abin yana da sosa rai. A can ne na fara wasa kuma ina girmama kungiyar."

"Filin wasan gidana ne - na san ina jin ina gida idan ina filin wasa na Old Trafford, amma Juve ma gidana ne."