Ina alfahari da Alex Iwobi - Unai Emery

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kocin Arsenal Unai Emery ya yabi dan wasan Najeriya Alex Iwobi kan yadda ya inganta wasansa tun lokacin da suka fara aiki tare a kakar bana.

Emery ya yabi dan wasansa ne kafin gumurzun da za a yi tsakanin Arsenal da Liverpool a Emirates a ranar Asabar.

Kocin ya shaidawa BBC cewa yana alfahari da dan wasan kan yadda ya inganta wasansa.

"Matashi ne muna bukatar kara masa kwarin guiwa ya kara gogewa saboda yana da inganci da zarafin taka leda," in ji shi.

Ya ce abin da Iwobi yanzu ke bukata shi ne a kara dora shi kan dabarun da zai kara ci gaba.

Labarai masu alaka