N'Golo Kante ya sabunta yarjeniyarsa a Chelsea

N'Golo Kante na Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption N'Golo Kante ya koma Chelsea ne a shekarar 2016

Dan wasan Chelsea N'Golo Kante ya sabunta yarjeniyarsa a kungiyar Chelsea inda zai ci gaba da wasa har zuwa shekarar 2023.

Dan wasan kasar Faransar, mai shekara 27, ya zura kwallaye uku ne a wasanni 81 da ya yi wa kungiyar a gasar firimiya.

Kante ya koma Chelsea ne a shekarar 2016 daga kungiyar Leicester City.

Chelsea ta lashe kofin firimiya tare da dan wasan kuma dan kwallon ya ci kyautar gwarzon kwararren dan wasa na shekarar.

Yana cikin jerin sahun 'yan wasa da suka ci kofin Firimiya a jere a kungiyoyi daban inda ya lashe kofin a Leicester kuma ya koma ya daga kofin a Chelsea.

"Shekaru biyu ne kyawawa kuma ina fatan kara samun nasarori," in ji Kante.

"Tun bayan da na koma Chelsea, na samu ci gaba a matsayina na dan wasa, na samu kyaututtuka da ban taba tsammani ba."

"Ina son garin, ina son kungiyar kuma ina farin cikin ci gaba da zama a nan."

Kante ya taka wa Faransa leda sau 36 kuma yana cikin 'yan wasan kasar da suka lashe kofin duniya a Rasha."

Daraktan Chelsea, Marina Granovskaia, ya ce: "Lokacin da muka sayi dan kwallon, mun fahimci cewa mun sayi muhimmin dan wasa - kuma ya ba kowa mamaki saboda yadda yake aiki tukuru, ba tare da nuna son kai ba."

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba