'Marcus Rashford na son ya koma Real Madrid'

Marcus Rashford
Bayanan hoto,

Rashford na son a dinga fara wasa da shi ko ya bar United

Dan wasan Manchester United Marcus Rashford ya ce a shirye yake ya fara tattaunawa da Real Madrid idan aka ci gaba da fara wasa ba da shi ba a Old Trafford, in ji jaridar (Sun)

Tun farkon kaka Real Madrid ke sanya ido kan dan wasan na Ingila mai shekara 21, musamman rawar da ya taka a wasan da Ingila ta doke Croatia 2-1 a ranar Lahadi.

Sun ta ce dan wasan ya ce bai taba tunanin zai iya barin United ba, kulub din da ya taimakawa ci gaban rayuwarsa.

Kocin Ingila Gareth Southgate ya shaida wa Rashford cewa makomarsa a tawagar Ingila ta dogara ne da rawar da yake takawa a kulub dinsa.

Jaridar ta ce Real Madrid tana tunanin karbo Rashford da kuma dan wasan Tottenham Christian Eriksen.

Kuma tuni Madrid ta tuntube shi ta hanyar wakilansa.

Darajar dan wasan dai ta kai fam miliyan 50, kuma zuwa karshen kakar badi ne kwangilarsa za ta kawo karshe a Old Trafford.