Real Madrid ta kwaso kwallo uku a Eibar

Eibar ta doke Madrid 3-0

Kungiyar Eibar ta doke Real Madrid da ci 3-0 a wasan mako na 13 a gasar cin kofin La Liga da suka kara a ranar Asabar.

Eibar ta ci kwallayen ta hannun Gonzalo Escalante a minti na 16 da fara tamaula, bayan da aka dawo daga hutu ne ta zura biyu ta hannun Sergi Enrich da kuma Kike Garcia.

Wannan ne karon farko da Eibar ta yi nasarar doke Real Madrid a dukkan karawa 10 da suka yi, ko a bara ma Real ce ta ci 3-0 a Santiago Bernabeu, sannan 2-1 a gidan Eibar.

Wannan ne karon farko da aka ci Santiago Solari tun bayan da Real ta ba shi aikin horar da kungiyar, bayan da ya ci wasa hudu a jere a matsayin rikon kwarya.

Wannan ne karo na biyar da aka doke Madrid a La Ligar bana, bayan Sevilla 3-0 da Alaves 1-0 da Levante 2-1 da wanda Barcelona ta ci 5-1 a Camp Nou.

Real za ta karbi bakuncin Valancia a wasan mako na 14 a gasar La Liga a ranar 1 ga watan Disamba, ita kuwa Eibar za ta ziyarci Rayo Vallecano a ranar 30 ga watan Nuwamba.