Sergio Ramos ya musanta yana shan abubuwan kara kuzari

Sergio Ramos na Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kaftin din Real Madrid Sergio Ramos ya musanta yana shan abubuwan kara kuzari bayan wani sakamakon bincike ya nuna ya karya ka'ida bayan wasan karshe a gasar zakarun Turai ta 2017 da aka buga a Cardiff.

Wata mujallar Jamus da ake kira Der Spiegel ta yi kirarin cewa binciken da aka gudanar kan dan wasan na Spain ya nuna cewa ya sha kwayar dexamethasone don kara kuzari.

"Na kyamaci kara kuzari, ban taba yi ba, kuma ba zan taba yi ba, ban yarda da shi ba, kuma ba zan taba yarda da ko wane irin nau'i na kara kuzari ba," in ji Ramos.

Sakamakon binciken Der Spiegel ya ce Ramos mai shekara 32 ya sha wasu kwayoyi na rage radadin ciwo kafin wasan karshe da Real Madrid ta doke Juventus.

Hukumar Uefa ta amince da sakon uzurin Ramos wanda ya dora laifin kan likitansa da ya harhada maganin.

Sai dai kuma likitan da ba a bayyana sunansa ba, a cikin wasikar da aka aika wa Uefa ya rubuta wani magani na daban bayan kammala wasan a rahoton gwajin da aka gudanar kan Ramos.

An shaida wa masu gwaji cewa an yi wa Ramos allurar maganin betamethasone a guiwarsa da kuma kafadarsa ta hagu, wanda kuma hukumar da ke yaki da shan abubuwan kara kuzari Wada ta haramta.

Labarai masu alaka