Shin zamanin Ronaldo da Messi ya wuce ne?

Messi na Argentina da Ronaldo na Portugal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsawon shekara 10 Messi da Ronaldo suna lashe Ballon d'Or

Ga alama kyautar Ballon d'Or ta bana za ta kawo karshen zamaninsu Messi da Ronaldo da suka shafe shekara 10 suna lashe kyautar tsakaninsu.

Rahotanni daga Faransa sun nuna cewa za a samu sabon gwarzon dan kwallon duniya a bana sabanin Messi da Ronaldo.

Tun makwanni biyu da suka gabata aka kwarmato cewa Luka Modric da Raphael Varane da Antoine Griezmann su ne 'yan wasa uku da suka fi samun maki, wadanda kuma cikinsu daya zai lashe kyautar Ballon d'Or.

Wasu rahotanni kuma sun ce dan wasan Paris St Germain Kylian Mbappe na cikin 'yan wasan guda uku da suka hada da 'yan wasan Real Madrid guda biyu Luka Modric da Raphael Varane.

Tuni dai Modric dan kasar Croatia ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai da kuma gwarzon dan wasan duniya na FIFA.

Wasu rahotanni kuma sun nuna cewa akwai yiyuwar Griezmann zai lashe kyautar Balon d'Or a bana.

Dan wasan ya lashe wa Faransa kofin duniya a Rasha bayan ya dauki kofin zakarun turai na Europa league.

Wani babban dan jarida da ke aiki da kafar wasanni ta beIN, kuma mai yi wa CNN da Gazetta dello sharhi ya ce wata majiya daga mujallar da ke bayar da kyautar ta tabbatar da Griezmann ne zai lashe kyautar a bana.

Babu sunan Ronaldo ko Messi daga cikin jerin 'yan wasan guda uku a karon farko cikin shekaru 10.

Ronaldo da Messi sun lashe kyautar sau biyar a tsakaninsu.

Kuma sau biyar suna take wa juna baya a matsayin na biyu tun 2007.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Messi da Ronaldo sun kafa tarihin da ba a taba kafawa ba a duniyar kwallon kafa

An dade ana muhawara game da 'yan wasan, kan wanda ya fi iya murza leda. Kuma ga alama muhawarar da aka jima ana yi game da 'yan wasan ta kawo karshe.

Tafiyar Ronaldo zuwa Juventus daga Real Madrid, wasu na ganin ya nuna alamar kawo karshen zamanin dan wasan da ya dade yana hamayya da Messi na Barcelona.

A ranar 3 ga watan Disemba ne za a yi bikin bayar da kyautar Balon d'Or a birnin Paris.

Wata mujallar kwallon kafa a Faransa ce ke bayar da kyautar duk shekara.