Ina Dembele zai koma idan ya bar Barca? Hazard ya fasa komawa Paris St-Germain

Ousmane Dembele Hakkin mallakar hoto Getty Images

An nemi dan wasan gaba na Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 21, ya bar Barcelona a lokacin da za a soma musayar 'yan kwallon kafa a watan Janairu kuma hakan ka iya bai wa Neymar damar komawa Nou Camp daga Paris St-Germain, in ji (Goal)

Manaja Marco Silva ya ce Everton na shirin gwada karfin son da Barcelona ke yi wa dan wasa mai shekara 25 Andre Gomes, wanda Goodison Park ya are shi, domin ya koma can dindindin. (Liverpool Echo).

Dan wasan Chelsea Eden Hazard, dan shekara 27, ya fasa komawa Paris St-Germain, ko da yake ya ce zai iya barin Stamford Bridge a bazara, in ji (Canal+ daga Goal).

Rahotanni sun ce daraktan Milan Leonardo na tattaunawa da Chelsea a kan dan wasan tsakiya Cesc Fabregas, mai shekara 31, da 'yan wasan baya Gary Cahill, mai shekara 32, da Andreas Christensen, dan shekara 22. (Football Italia).

Manchester United ya aika da 'yan wasanta da ke rukunin matasa domin kallon wasan da dan wasan West Ham Declan Rice, mai shekara 19, a fafatawar da Manchester City suka doke Hammers da ci 4-0 ranar Asabar, in ji (Metro).

Dan wasan Barcelona Jordi Alba, dan shekara 29, ya ce bai sabunta kwantaraginsa ba, don haka babu tabbas a kan makomarsa, in ji (ESPN).

Manchester United ka iya jira domin sayen dan wasan Roma dan shekara 22 Lorenzo Pellegrini bayan da kulob din ya fahimci cewa zai iya yin amfani da wata dama ta sayen sa a karshen kakar wasa ta bana, in ji (Mirror daga Manchester).

Manajan Newcastle Rafa Benitez ya ce ba zai fitar da ran sake komawa Serie A ba nan gaba idan ya gaza cimma burinsa a St James' Park, in ji (Newcastle Chronicle).

Labarai masu alaka